Haɗin gwiwar Sin da Afrika kan tattalin arzikin zamani ya bai wa Afrika damarmaki masu kyau

Daga MINA

Abokai, yanzu ana gudanar da babban taron yanar gizo na duniya a ƙasar Sin.

Bunƙasuwar Sin a wannan fanni ya amfanawa duk fadin duniya.

Yau “duniya a zanen MINA” zai yi muku bayani kan ma’anar hadin kan Sin da Afrika a fannin tattalin arzikin yanar gizo.

Taron da ake gudanarwa a birnin Yiwu dake lardin Zhejiang ya samu halartar wakilai fiye da 2000 daga ƙasa da ƙasa, kuma babban abin da ake tattaunawa a taron shi ne hadin kai da samun ci gaba tare.

Bisa ƙididdigar da hukumar kula da masana’antu da sadarwa ta ƙasar Sin ta bayar, an ce, yanzu Sin ta ƙulla yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninta da ƙasashe 17 dake kan hanyar siliki ta fannin yanar gizo, kuma ta kafa tsarin hadin gwiwa da ƙasashe 23 dake kan wannan hanya a fannin kasuwanci ta yanar gizo.

Alƙaluman da kwamitin kula da sadarwa na Najeriya ya bayar, sun yi nuni da cewa, ya zuwa watan Yuni na bana, yawan mutanen dake kama Intanet ya haura miliyan 150, wato kaso 70% na al’ummar ƙasar na samun hidimar yanar gizo.

Irin waɗannan sauye-sauye da aka samu ba su rabuwa da ababen more rayuwa da kamfanonin Sin ke taimakawa wajen gina su a ƙasar ta fannin yanar gizo.

Cikin ‘yan shekarun baya, kamfanonin Sin sun himmantu wajen kafa na’urorin yanar gizo a Afrika.

Alal misali, zuwa ƙarshen watan Oktomba da ya wuce, kamfanin ZTE na ƙasar Sin ya baiwa ‘yan Afrika fiye da miliyan 400 hidimar yanar gizo, ta hanyar gina na’urorin yanar gizo.

Yanzu ana iya samun sadawar 5G a nahiyar Afrika, matakin da ya baiwa tattalin arzikin yanar gizo tushen samun bunkaysuwa mai kyau, shi ya sa mutane da dama suka samu arziki ta hanyar dogaro da yanar gizo.

Wata takardar bayani kan bunƙasuwar tattalin arzikin yanar gizo a Afrika da aka fitar a watan Mayun bana ta yi nuni da cewa, a shekarar 2019 yawan mutanen da suka kama ayyukan da suka shafi cinikayyar yanar gizo ya ƙaru zuwa miliyan 233, adadin da kuma zai kai miliyan 478 kafin shekarar 2024.

Haɗin kan Sin da Afrika a wannan fanni mai haɓaka, ya kuma ingiza cinikayyar Sin da Afrika zuwa gaba.

Bisa alƙaluman da aka bayar, an ce, yawan kuɗin dake shafar cinikin ɓangarorin biyu ya ƙaru da kashi 35% a shekarar bara, kuma tattalin arzikin yanar gizo ya zama sabuwar hanyar kawar da talauci a nahiyar Afirka.

A halin yanzu, ƙasashen Afrika da dama na sa ran yin haɗin gwiwa da kasar Sin a fannin tattalin arzikin yanar gizo, hakan ya sa wasu kamfanoni masu ƙarfi na ƙasar Sin a wannan fanni suka haɗa kai da ƙasashen Afrika ciki har da Najeriya, don taimaka musu wajen samun ci gaba dangane da tattalin arzikin yanar gizo a fannin hada-hadar kuɗi da ciniki ta yanar gizo da sufurin kayayyaki da sauransu.

Nahiyar Afrika na da ƙasashe maras ci gaba mafi yawa a duniya, kuma yadda ƙasar Sin ta ba da taimakon ingiza bunƙasuwar bisa haɗin gwiwar tattalin arzikin yanar gizo, ba shakka zai samar da sabbin damammaki masu kyau ga nahiyar wajen kawar da talauci, baya ga haka zai ingiza bunƙasuwar tattalin arizkin duniya gaba ɗaya.

Mai zane da kuma rubutawa: MINA