Bayan biyan malaman jami’a rabin albashi, ASUU ta ce ba za ta sake tsunduma yajin aiki ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Malaman Jami’a ASUU, ta ce ba za ta kuma komawa sabon yajin aiki ba duk da gwamnati ta saɓa alƙawarin da ta ɗauka musu.

Gwamnatin Nijeriya ta biya ASUU albashin rabin wata bayan da ta janye yajin aikin watanni takwas da ta shiga a watan Fabrairu.

Ƙungiyar ta yi zama, ta kuma yi Allah-wadai da abin da Gwamnatin Nijeriya ta yi mata a makon da ya gabata.

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ta kammala zamanta na Majalisar Zartaswa, inda ta yanke ba za ta sake shiga wani sabon yajin aiki ba a nan kusa.

Sai dai, ƙungiyar ta yi Allah wadai da yunƙurin Gwamnatin Tarayya na son sake tunzura mambobinta ta hanyar biyansu rabin albashi na watan Oktoba.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Talata bayan kammala zaman NEC, Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, malaman jami’a masu ilimi ne ba wai ma’aikata gama gari ba.

A nata ɓangaren, Gwamnatin Tarayyan ta yi bayanin cewa ta biya malaman albashi ne dogaro da kwanakin da suka yi suna aiki a watan.

Sai dai Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke, ya mayar da martani cewa mambobinsu ba ma’aikatan wucin-gadi ba ne kuma bai kamata a dinga yi musu tamkar irin waɗannan ma’aikatan ba.

Osodeke ya kwatanta abinda gwamnatin ta yi da karantsaye ga dokokin da aka ɗauke su aiki a kai.

Ya ce Majalisar Zartarwa ta ƙungiyar sun bayyana mamakinsu kan yadda aka mayar da malaman tamkar ma’aikatan wucin-gadi wanda hakan bai taba faruwa ba a tarihin jami’o’i ba.

“Ƙungiyar ASUU ta janye yajin aikinta na tsawon wata takwas a ranar 14 ga watan Oktoban 2022 domin biyayya ga umarnin Kotun Masana’antu da kuma biyayya ga wasu jiga-jigan ‘yan Nijeriya kamar su Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.

“Matakin da ƙungiyar ta ɗauka alama ce ta yarda da fannin shari’a kuma sauran cibiyoyi da rassan gwamnati da saka buƙatar ‘yan ƙasa gaba da komai.

“Wannan mun yarda a matsayinmu na masu tunani, fasaha da kishin ƙasa, ba wai za mu taimaka kawai wurin kwantar da tarzoma ba, amma za mu saka tabbatar da alaƙa mai kyau tsakanin gwamnati da ma’aikatan Nijeriya bakiɗaya.

“Sai dai kuma, martanin gwamnatin ga ASUU kan albashin da aka biya na kwanaki 18 na watan Oktoban 2022, ya ayyana mu a matsayin ma’aikatan da ake biya kullum.

“Wannan ba take doka ba ne kaɗai, wannan ya haɗa da karantsaye ga dukkan dokokin ɗaukar aiki na malamai a dukkan duniya,” cewar Osodeke.

Osodeke ya yaba wa lakcarorin kan jajircewarsu tare da kira ga ɗalibai da iyayensu da su kasance masu fahimta yayin da ASUU ke ƙoƙarin sasanci tare da kiyaye doka.

Ya ce a taron gaggawar da Majalisar Zartarwa ta ASUU ta yi a ranar Litinin, ƙungiyar ta zanta ne tare da tattaunawa kan dakatar da yajin aikin.