Abba Gida-Gida ya shawarci shugabanin ƙananan hukumomin da za a gudanar da zaɓen cike giɓi a yankinsu

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya sake bai wa shugabannin ƙananan hukumomin jihar kano 44 da sauran manyan ma’aikatansu shawarar kauce wa kuskuren yin amfani da su wajen ɗibar kuɗaɗen ƙananan hukumomin kan zaɓen da za a sake a wasu yankuna a jihar.

Wannan batun na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kakakin sabon Gwamnan, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, Gwamnan mai jiran gado na da cikakkiyar masaniyar cewa gwamnati mai barin gado tana shirin fitar da kuɗaɗe da adadinsu ya kai kusan sama da Naira miliyan 60 domin yin amfani da su wajen ɗauko ‘yan daba don su tada zaune tsaye yayin da za a gudanar da zaɓukan da za a sake a wasu kananan hukumomi da ke jihar.

Dawakin Tofa ya ƙara da cewa, suna kira ga duk shugabannin ƙananan hukumomi musamman na Nasarawa da Doguwa da su kiyaye bada kuɗaɗen saboda gwamnati mai jiran gado ba za ta lamunci ɓarnatar da kuɗaɗen al’umma ba gaira babu dalili ba.

“Ina mai amfani da wannan damar dan sanar da ku cewa, duk waɗanda wannan shawarar ta shafa da su kwana da sa ni cewa duk wanda ya bari aka fitar da kuɗi da saninsa to ya sani za mu ɗauki matakin da ya dace da zaran an rantsar da sabuwar gwamnati.”

Idan dai za a iya tunawa a Jihar Kano akwai kusan ƙananan hukumomi 16 da aka samu matsala yayin da zaɓen da ya gabata da ya haɗar da na ‘yan Majalisar Tarayya biyu, Fagge da ƙaramar hukumar Doguwa, sai majalisar jiha 14, wanda adadin akwatuna 206 ne za a canza zaɓen.

Wa su daga cikin ƙananan hukumomi kamar yadda hukumar zaɓe ta Jihar Kano ta fitar sun haɗa da Ƙaram Hukumar Danbatta, Makoda, Dawakin Tofa, Gabasawa, Gezawa, Gaya, Takai da kuma Garko.

Sauran su ne ƙananan hukumomin Wudil, Warawa, Ungoggo, Ajingi, Gwarzo, Tudun Wada da kuma Fagge.