Duk da wadatar takardun Naira masu POS na cajin wuce hankali

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu masu sana’ar POS su na cigaba da cajin abokan cinki fiye da kima duk da wadatar takardun Naira a Nijeriya.

An gano cewa wasu masu POS a Babban Birnin Tarayya, FCT, na caji tsakanin Naira 300 zuwa N200 kan Naira 5,000 da aka cire.

Romanus Chukwu, wani abokin ciniki da aka gani a ɗaya daga cikin wuraren da ke Nyanya, ya ce, har yanzu cajin yana da yawa idan aka kwatanta da lokacin da takardun kuɗi suka yi ƙaranci.

Chukwu ya yi kira ga masu sana’ar da su koma karɓar Naira 100 da aka saba biya duk Naira 5,000 zuwa N10,000 da aka cire.

A halin da ake ciki, wani mai POS a Nyanya wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, har yanzu tsadar kuɗi bai wadata ko ina ba, wanda hakan ya sa su ke caji mai yawa.

NAN ta ruwaito cewa CBN ya ce zai janye lasisin jami’an POS da aka samu da laifin ƙara caji kan kwastomomin da ke cire kuɗi a wajensu.