Abin da cire tallafin wuta ya jawo mana

Daga SHAMSUDDEEN MUHAMMAD

Wannan rubutu labarin karan kaina ne, na abin da ‘yan hukumar rarraba wutar lantarki (KEDCO) suke min a yanzu haka. Kuma yana da kyau mu san gidana mutum 4 ne kacal a ciki, biyu manya biyu yara, don haka wutar da muke amfani da ita ba ta da yawa.

Hasali ma firji ne kaɗai yake jan wuta a gidan, shi ma kuma sai mu yi kwana 4 ba wuta mai karfin da za ta iya kunna shi. Sannan kuma ba a saka mana mita ba, don haka, bill ake kawo min duk wata (postpaid billing).

Na yi wannan shimfiɗar ne domin a fahimci maudu’i da kuma muhallin maganata.

A haka KEDCO ta rubuto min bill din Naira 17,364.37 na watan Maris na 2023, watan da kowa ya shaida ba su bayar da wutar arziki ba.

Yadda aka yi wannan kuɗi ya Kai haka:
Kudin wuta: sun ce na sha wuta ta awoyi 230KW a watan, kowacce awa ɗaya akan kuɗin Naira 70.23 wanda idan ka lissafa adadin kuɗin ya zama Naira 16,152.90
Sannan harajin VAT da zan ba wa Gwamnati saboda na sayi wuta da kuɗina: N1,211.47 (7.5% kenan).
Jimilla: N17,364.37. Haka aka rubuto min.

  1. Da farko dai awoyi 230 KW da aka rubuto min, su ma sun san ba haka ba ne, domin wannan yana nufin a kwana 31 na watan Maris 2023, kullum mun sami cikakken kilowatt na awa 7 da rabi (7.5 KWH per day), wannan kuwa ni dai na San ba haka ba ne. Akwai lokacin da muka yi kusan awa 50 (Kwana 2) babu wuta a cikin watan.

Lokacin da ake kawo wutar Kuma ba ta yin awa 7 a rana, ko da ta yi awa 7 ƙarfinta bai Kai kilowatt ba, domin kuwa wani lokacin ko farin florescent mai 10 watts ba ya iya kamawa. Maimakon cikakken kilowatt a awa ɗaya, wutar ba ta wuce rabin KWH (500 watts per hour ko Kuma abinda muke cewa half current). Don haka ko da an kawo wutar awa 7 a rana, ka ga tana dai-dai da 3.5KWH kenan a kullum. Abin tambayar shi ne, me ya sa KEDCO take wannan aringizon awoyin? Na farko kenan.

  1. Na biyu, kowacce awa ɗaya ina biyan N70.23 ta wannan wutar manja (half current) din; Innaa lillahi wa Inna ilaihi rajiun. Idan ka saka ƙaramin generator Tiger, ka zuba masa litre guda (N195/litre idan ka samu Mai a NNPC Filling station ko TOTAL) zai iya yi maka 3 hours, ka ga N65 kenan duk awa ɗaya; amma wutar KEDCO N70.23 duk awa guda, Kuma fa ban haxa da harajin VAT (7.5%) ba! Idan ka hada da VAT wuta ta tashi a N75.50 duk awa daya.

Kuma sau da yawa ma abinda wutar Tiger za ta yi maka ta KEDCO ba za ta yi ba. A ce wannan yana faruwa ne a ƙasar da ta fi kowacce yawan talakawa a duniya?! Sannan kuma mu na biyan haraji ga Gwamnati? Kuma duk shekara ana kasafta Biliyoyin kuci ga harkar wutar lantarki? Haba jama’a!

  1. Baya ga haka, duk wannan aringizon kuɗi da KEDCO za ta yi maka, sai ka biya Gwamnati 7.5% na wannan kuxin. Don haka, yawan kuɗin wutar da ka sha, yawan harajin da za ka biya. Gwamnati, ta kasa bayar da wuta kyauta, Gwamnati, ta daina bayar da tallafi wuta ga talaka, Gwamnati, ta kasa daidaita farashi a kan abinda DISCOS suke cajs na kuɗin wutar, sannan kuma ta ɗora wa talaka haraji a kan wutar da zai siya da kuɗinsa; Wannan wane irin zalunci ne? Ina zaton ko Fir’auna bai yi wannan kalar muguntar ba.
  2. Shi dama jari hujja (monopoly) matsalarsa kenan, babu cigaba sai cutar da talaka. Shi ne dalilin da ya sa Musulunci ya hana ka ƙirƙiro monopoly da gangan, domin yana jawo muna-muna a kasuwa da kuma cutarwa. To ga shi dai, Gwamnatin Jonathan ta yi cefanar da wuta shekara 12 kenan idan ban manta ba, babu wani cigaba. Kuma har gobe Gwamnati tana kashe tiriliyoyi a kan samar da wuta, ba abinda ya chanja.

Sannan Gwamnatin Buhari ta zo ta cire tallafin wutar gabaɗaya, rashin amfani duk ya dawo kan talaka. Kuma ga shi babu wani fata ko kusa, ko nesa. Kawai an damƙa mu a hannun azzaluman DISCOS, yadda Suka dama, haka za mu sha. Ko muna so, ko ba ma so. Hasbunallah wa ni’imal Wakeel!

A ƙarshe, nake cewa, Allah Ya tsine wa Mai ƙarya, Kuma Allah Ya isa ban yafe ba.

Mutane da da ma a sun ba ni shawarar na koma tsarin wutar kati ta mita. Amma a inda gizo ke saƙar shi ne, idan na yi hakan, matsala guda tak, na iya magancewa, wato matsalar yawan awoyi. Sai dai ya za mu iya warware sauran matsalolin kamar haka:

  1. Harajin VAT a kan wutar lantarki.
  2. Rashin ba da wadatacciyar wutar lantarki.
  3. Tirilliyoyin da ake kwasa daga lalitar al’umma a na a zubawa a harkar wutar lantarkin ƙasar ba tare da an gani a ƙasa ba.
  4. Tsawwala haraji.
  5. Jari hujja tatike al’umma.
    Waɗannan matsalolin su ne manyan matsalolin da ya kamata mu tunkara don gyarawa, a matsayinmu na al’umma.

Shamsu Muhammad, masanin tattalin arziki ne, kuma Malami ne a fannin tattalin arziki a Jami’ar Bayero. Ya rubuto daga Kano.