Daga FATUHU MUSTAPHA
Na ga babban abinda ‘yan Kwankwasiyya suke yaƙar Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da shi shi ne, wai zai yanka filaye da a ce ya ci zave, to amma ga wasu tambayoyi:
Waye ya yanka maƙabartar Kukar Bulukiya aka yi gidan mai? Ko nan ma Ganduje ne?
Wa ya rushe Badala, da sunan zai yi titi, ko shi ma Ganduje ne kawai ya tava yi?
Waye ya raba Daula Hotel ga maƙarrabansa? Shi ma Gwamna Ganduje ne?
Shin kantinan da aka gina a kan ganuwar da ke Ƙofar Mata ma Gwamna Ganduje ne ya yanka su?
Waye ya yanka filayen KERD ya sayarwa maƙarrabansa, su ma Ganduje ne?
Shin ofishin da Abba yake ciki, a gado ya same shi, ko a hannun wane dillalin ya saya?
Shi gidan da Aminu Abdussalam yake ciki, gonar su ce ta gado ya gina ko fili ne ya saya ya gina?
Waye ya kashe wuraren shaƙatawa na Green Zones na Kano ya yi gini a cikinsu. Ni dai na san Lambun shaƙatawa na Maiduguri Road da ke kusa da Almu Hospital ba a lokacin Ganduje aka sare shi ba.
Haka Lambun shaƙatawar da ke daura da Gidan Sarki na Nasarawa, inda Pizza Hut take a yanzu, shi ma ba a lokacin Ganduje aka yanka shi ba.
Ashe kafin Ganduje ma ana wa-ka-ci-ka-tashi da filayen gwamnati.
Allah ya ba mu shugabanni nagari, ya bai wa Gawuna sa’a a zave mai zuwa, ya sa shi ne mafi alheri.
Fatuhu Mustapha, marubuci ne, mai nazari da aharhi kan lamurran yau da kullum. Ya rubuto ne daga Abuja.