Abin da maigidanki ya shuka kika girba, ra’ayin ‘yan Nijeriya kan urwagidan Gwamnan Bauchi

‘Yan Nijeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu a soshiyal midiya dangane da halin da uwargidan Gwamnan Bauchi, Hajiya Aisha Bala Mohammad, da tawagrata suka tsinci kansu a lokacin da ta kai ziyara yankin Jamdan don ƙaddamar da cibiyar kula da lafiya.

Hotunan da suka karaɗe kafafen sada zumunta na zamani sun nuna yadda Aisha Bala da tawagarta suka sha fama a hanya saboda rashin kyawun hanyar zuwa garin da suka kai ziyarar.

Lamarin da ya kai matar Gwamnan ta sauka a motarta ta taka da ƙafafunta saboda matsalar caɓi a hanyar.

Tuni dai wasu ‘yan Nijeriya suka yi ra’ayin halin da Aisha Bala ta tsinci kanta daidai ne tun da rashin bai wa yankin kulawa daga gwamnatin da maigidanta ke jagoranta ya haifar da hakan.

Wasunsu kuwa cewa suka yi, abin da maigidanta ya shuka shi ta girba, don haka wannan daidai ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *