Alƙali, tsammani bai yi yadda PDP da LP su ka yi tsammani ba!

Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Babban alƙalin da ya jagaoranci ƙarar ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban Nijeriya na ranar 25 ga watan Febreru 2023 Haruna Tsammani bai yanke hukunci bisa yadda manyan jam’iyyun adawa biyu PDP da LP da kuma ta uku APM su ka yi tsammanin samun nasara ba. Dama haka shari’a ta ke kuma ba a hasashen me alqali zai yanke hukunci sai an jira ya yanke bisa yadda ya ke a tanadin doka.

Hasalima kotu kan iya kama mutum da raini matuƙar ya ambaci wani tunani na abun da ya ke ganin zai faru a kotun. Amma dai aƙalla za a iya tsammanin fatar samun nasara kamar yanda waɗannan jam’iyyu da a ka fafata da su a zaɓen su ka shigar da ƙara don rashin amincewa da sakamakon zaɓen da shugaban hukumar zaɓe Farfesa Mahmud Yakubu ya ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Yanzu ga shi ma har gwamnatin ta yi kwana 100 cur a kan karaga. Ai kamar shekaranjiya ne tsohon shugaba Buhari ya hau karagar mulki a 2015 bayan fafatawa na tsawon shekaru 12 da ma zuwa kotu na watanni kimanin 30 da ya kan ambata da kan sa. Yau shugaba Buhari ya zama sai dai tarihin ya zama shugaban mulkin farar hula ba ya ga na soja da ya yi a can baya.

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban Nijeriya ta yi watsi da karar masu ƙalubalantar aiyana shugaba Bola Tinubu a amtsayin wanda ya lashe zaɓen 25 ga watan Febreru.

Babban alƙali da ya jagoranci alƙalan kotun 5 Haruna Tsammani ya ce ba ko daya daga zargin aibun zaɓen da masu ƙara su ka tabbatar da sahihan hujjoji. Ƙalubalen ya haɗa da shari’ar safarar miyagun ƙwayoyi a Amurka ga Tinubu, tsaida Kashin Shettima takara alhali ya na takarar majalisar dattawa, rashin cika ƙa’idar samun ƙuri’un da za su ba shi damar lashe zaɓe.

Gabanin waɗannan ma akwai zargin hukumar zaɓe ta ki amfani da sakamakon na’urar tura sakamakon zave ko rashin wallafa sakamakon a manhajar sakamako sai a ka yi amfani da sakamakon da wakilan zaɓe su ka taho da shi. Wakilin PDP Dino Melaye tun a ɗakin tattara sakamkon ya yi watsi da yadda shugaban hukuamr Mahmud Yakubu ya tafiyar da amsar sakamakon. Melaye bai ma tsaya sai an kammala bayyana sakamako ya jagoranci ’yan hamaiya su ka fice daga ɗakin.

Alƙalai 2 cikin 5 din gabanin yanke hukuncin ma sun mara baya ga babban alƙali tsammani don haka ko da sauran biyu sun yanke hukuncin da ya sha bamban ba wani abu da zai sauya. Tsarin shari’a kenan da kan yi amfani da rinajye shi ya sa alƙalai kan zama 5 ko 7 amma dai babban abu ya zama waɗanda su ka fi rinjaye ko da huɗu ne su ne za a yi amfani da hukuncin su. Ma’ana in huɗu ne a na buƙatar 3 su yanke hukunci don nasara kan ɗaya.

A dai hukuncin kotun ya nuna masu ƙara da su ka haɗa da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Leba sai dai su garzaya kotun koli don ƙalubalantar hukuncin. Tsarin na farawa ne daga kotun ɗaukaka ƙara da kan zama ta farko sai kuma tafiya ƙoli da kan zama ta ƙarshe har masu salon magana ke ma ta kirari da kotun Allah ya isa don daga nan sai dai haƙuri ko a koma sabuwar shari’a daga matakalar kotuna.

Ba a tava samun yanke hukunci a Nijeriya da ya sauke shugaban da ke kan gado ba, amma an samu hukunci da ya sauke wasu gwamnoni da ma ’yan Majalisar Dattawa da wakilai. A ma Afurka gaba ɗaya kamar yadda masanin siyasa Farfesa Hussaini Tukur ya ce a Kenya ne kaɗai a ka taba samun kotu ta yanke hukuncin da ya kawar da shugaba daga kan gado.

Tuni jam’iyyar Leba ta Peter Obi ta yi watsi da hukuncin kotun ƙarar zaɓen shugaban Nijeriya ta yanke na tabbatar da nasarar shugaba Bola Tinubu.

Leba ta ce sam hakan ya sabawa muradin jama’a daga irin murɗiya da a ka yi lokacin zaɓen da kowa ya gani ƙarara. Leba a martanin da kan yi mai tsauri ta ce tamkar fashi a ka yi wa dimokuraɗiyya.

A nan Leba ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an tabbatarwa mutane abun da su ka zaɓa ta hanyar gaskiya.

Hakanan Leba ta ce dimokraɗiyya za a tausayawa ga yanda a ka yanke hukuncin, kuma za ta nazarci hukuncin bayan tattaunawa da lauyoyi don sanin matakin ɗauka. Ba tare da wata-wata ba ma jigo a tafiyar Obi wato Aisha Yesufu ta zayyana hukuncin da tamkar wasan kwaikwayo a ka shirya. Duk da ta ce Nijeriya ta dukkan ’yan Nijeriya ce amma ita sam shugaba Tinubu ba zai taɓa zama shugaba a wajen ta ba.

Yesufu ta koka cewa kotu ta nemi hukumar zaɓe ta kawo kayan zaɓe don a duba amma hukumar ba ta kawo ba; da hakan kuma bai sa kotun ɗaukar mataki ba sai korar ƙarar. A na sa ɓangare shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Umar Gnaduje a siyasance ya maida martanin farin cikin nasarar ya na mai cewa ta kan yiwu kenan waɗanda ba su gamsu da hukuncin ba su ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli.

A nan ya nuna a je zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Mataimakin shugaba Tinubu wato Kashim Shettima da ya halarci zaman kotun ya nuna farin ciki da cewa yanzu shari’a ta kare don haka gwamnatin su za ta cigaba da aikin ta har ma ya dau alwashin nan ba da daɗewa ba wahala ko quncin tattalin arzikin da mutane ke ciki zai yi sauki. Shettima ya hakkake a bayanin sa cewa shugaba Tinubu na da tausayi kuma ya na da kyakkyawar manufar inganta rayuwar ’yan Nijeriya.

Tsammanin ’yan hamaiya da su ka shigar da ƙara na su na sa ran adalci da zai zama an kawar da Tinubu daga mulki bai samu nasara ba. Farko dai kotun sauraron ƙarar sakamakon zaɓen shugaban Nijeriya na 25 ga watan Febreru ta aiyana za ta yanke hukunci ranar Larabar da ta gabata.

Matakin kotun ya zo ne bayan kammala sauraron jawaban ƙarshe na sassan da ke cikin ƙarar a watan jiya.

Yanke hukuncin ya zo ne mako biyu gabanin cikar wa’adin kwana 180 na ƙa’idar sauraro da yanke hukuncin bisa doka kuma ya shafi jam’iyyar PDP, Leba da APM da ke buƙatar kotun ta soke ayyana Bola Tinubu da hukumar zave ta yi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa PDP Atiku Abubakar da mai bi ma sa baya a yawan ƙuri’u Peter Obi na Leba na zayyana zaɓen a matsayin wanda a ka nuna murɗiya da ƙin amfani ko bayyana ainihin sakamakon na’urar tattarawa da aika sakamako.

Lauya mai zaman kan sa a Abuja Barista Mainasara Kogo Umar ya ce koma yaya shari’ar ta kaya duk wanda bai gamsu ba na da damar garzayawa kotun ƙoli.

Kakakin shugaba Tinubu Ajuri Ngelale ya ce shugaban ya na da ƙwarin gwiwar samun nasara a sakamkon shari’ar.

Shi kuma ɗaya daga manyan jami’an kamfen na PDP Alhaji Yusuf Dingyadi ya ce sun gabatar da duk hujjojin da su ka dace don neman kawar da Tinubu daga fadar Aso Rock.

A na sa ɓangaren kakakin kamfen ɗin jam’iyyar Leba Yunusa Tanko ya yi zargin katsalandan a shari’ar amma ya ce hankalin su a kwance ya ke bisa hujjojin da su ka bayar.

An gabatar da zaman yanke hukuncin kai tsaye ta gidajen talabijin don biyan muradun jama’ar ƙasa.

Mai amasa kara wato gwamnatin Nijeriya ta baiyana ƙwarin gwiwar samun nasara kuma tsammanin ta ya tabbata.

Baya ga sanarwa ta musamman daga kakakin shugaban Ajuri Ngelale na kwarin guiwar samun nasara, mai ba wa shugaban shawara na musamman kan siyasa Ibrahim Kabir Masari ya ce ba sa shakka ko kokonton samun nasarar ƙarar.

“Aikin gama ya riga ya gama. Allan da ya ba da wannan nasara ga lokacin zaɓe shi zai ƙara tabbatar ma na da ita a lokacin shari’ar.”

Ita ma jam’iyyar sa APC ta bakin sakataren ta na labaru Felix Morka ta ce Tinubu ya lashe zaɓen na 25 ga watan Febreru don haka su na da ƙwarin gwiwar kotun za ta tabbatarwa Tinubu nasarar sa.

Yayin da kotu dai ba a yi ma ta shishshigi ko hasashen hukuncin da za ta yanke bisa ƙa’idar doka; a shari’un da a ka yi a baya tun fara wannan dimokuraɗiyya a 1999 ba a taɓa soke zaɓen shugaban ƙasa a naɗa wani ko a sake zaɓen ba.

In za a tuna a kotun ƙoli a zaɓen 2007, alƙalai 7 ne su ka yanke hukuncin ƙarƙashin marigayi Jostis Idris Legbo Kutigi. An samu canjaras na alƙalai 3 su ka soke zaɓen marigayi Umaru ’Yar’adua yayin da uku su ka ce zaɓen ya yi daidai. A nan dai Kutigi ya raba gardama da quri’ar sa ya marawa masu cewa zaɓen ya yi daidai baya.

Kammalawa;

Tun yanzu Tinubu ya samu nasarar a kotu ƙarar zave; PDP da Leba a haɗa da APM za su ɗaukaka ƙara ne ko kuwa a’a, a fili akwai logar ’yan siyasar Nijeriya da ke fatar lashe zaɓe ko ta halin kaka in ya so a kai su kotu don tunanin iya ruwa fidda kai; in kuma abokin hakaya shi ma ya iya ruwa sai a gwada ma sa iya laka. Kotun ƙoli ita ce ta Allah ya isa ko an gamsu ko ba a gamsu ba hukuncin ta bisa doka shi ne kankat. Shin kotun ƙoli ne ko shiryawa don 2027 in Allah ya kai rai?