Talakan Nijeriya bawan Allah

Gaskiya duk abin da tsohon Sarkin Kano Sunusi ya faɗa za a cigaba da shan wahala a Nijeriya alamu sun nuna biri ya yi kama mutum sai ko Allah ya kawo mafita da tallafin sa. Saboda tun gwamnatin da Tinubu ya gada vata shekara ba aka ce sai kowa ya ji a jikinsa aka yi wa gwamnati uzuri ana gani kamar wahala mai karewa ce daga ƙarshe za a sha jarmiya, amma alƙawari Bai cikaba.

Aka gama shekara huɗu aka sake uzuri aka zave su wahala ta cigaba. Har aka zo kan batun janye tallafin karatu ga ɗalibai da canjin kuɗi da janye tallafin mai da na hasken lantarki da cigaba da rufe iyakokin ƙasa inda mutane da dama suka rasa abin yi a fannin kasuwanci da sana’a tun daga kan iyakokin Nijeriya har zuwa cikin kasa wahala ta ninka mutane suka galabaita, wajen neman abinci ko da tsiya ko da arziki da yawa suka kauce hanya. Masu kuɗi da shugabanni suna kudancewa talakawa na tsiyacewa.

’Yan siyasa suka nemi a dakatar da janye duk wani tallafi sai an yi zaɓe, aka daga zuwa watan June.

Kuma tun farko Tinubu ya yi kamfen zai ɗora daga inda ya samu kuma mutane aka makance aka zaɓe shi. Ranar karɓar mulki ko ofis bai shiga ya nemi sanin damuwar ƙasar ba yace ya janye tallafin mai aka sake janye na karatu, abubuwa suka sake taɓarɓarewar madadin a ce lallai janye tallafin mai matsala ce an mai da shi sai aka sake faɗawa ruɗanin ba da tallafin rage raɗaɗi.

Gwamnoni da masu kuɗi suka kutsa kasuwanni suka ci gaba da cuwa cuwar saye kayan buqata komai ya yi tsada. Sana’a ta shiga garari abin da akasarin mutane ke samu bai kai suci abinci ko su biya kuɗin abin hawa zuwa wajen aiki ba komai ya sake DAGULEWA.

Tsakani da Allah yaushe ne za a ce akwai alamun samun saukin rayuwa a irin wannan yanayin da shiganni suka zamo basa ji basa ganin mawuyacin halin da mutane suka shiga kullum Kara matsesu ake yi. Komai Nisan jifa ƙasa za ta faɗi mu cigaba da addu’a Allah ya kawo mana nasa tallafin ya bamu mafita.

Wata uku da kwanaki Mulkin shugaban ƙasa Bola Tinubu Amma ba abin da ya canza sai wahala, saboda tun farko an assasa wahala an saita komai kan janye duk wani tallafi mai amfani ga talaka. Kuma bai ɓoyeba ya ce zai ɗora daga inda ya samu. Yanzu ta bayyana an janye tallafin mai an kuma gane tun farko talaka ke amfana da tallafin ba wasu masu kuɗi ba to, me ya sa ba za a maida tallafin ba.

Matuqar Tinubu yana son ya Mulki Nijeriya dole a matsayin sa na mai riƙe da wuƙa da nama na ragamar jagorancin ƙasa sai ya nemi masa sun zauna an soke duk wasu miyagun manufofin tattalin arziki da gwamnatin da ya gada ta shimfiɗa ya sa talakawa da tausayi a gaba shine mulkinsa zai ɗore.

Daga Muazu Hardawa Edita Jaridar Alheri Bauchi. 08062333065.