Biden ya jinjina wa Tinubu kan kare martabar dimokuraɗiyya

Shugaba Joe Biden na ƙasar Amurka, ya yaba da shugabancin da Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ke yi wa ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS).

Biden ya jinjina wa Tinubun ne la’akari da ƙoƙarin da ke ECOWAS ke yi wajen maido da tsarin mulkin dimokraɗiyya a ƙasar Nijar.

Biden ya ce jajircewar da Tinubu ke yi wajen kare tsarin dimokuraɗiyya a Nijar da ma yankin Afirka ta Yamma baki ɗaya abin a yaba ne.

Ya byyana haka ne yayin ganawarsu da Tinubu a wajen taron G20 da ya gudana a Delhi, Kasar Indiya.

Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, Fadar White House ta ce, “Shugaba Biden na maraba da matakin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka na ƙoƙarin inganta tattalin arzikin Nijeriya.

“Ya kuma yi wa Tinubu godiya dangane da shugabsncinsa a matsayin jagoran ECOWAS wajen kare martabar dimokuraɗiyya a Nijar da ma yankin Afirka ta Yamma.”