Matsalar tsaro: Wa’adin shekara guda

A kwanakin baya ne shugaban ƙasa Ahmed Bola Tinubu ya bai wa ministocin tsaro da hafsoshin tsaron Nijeriya wa’adin shekara guda domin kawo ƙarshen duk wani nau’in rashin tsaro a ƙasar. Da yake fuskantar ƙalubalen, Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya ziyarci wasu manya-manyan hafsoshin soji domin jin yadda za a ɓullo wa bakin zaren.

Kafin yanzu dai an fara samun tashin hankali sakamakon yawaitar hare-haren ta’addanci da kashe-kashe a wasu sassan ƙasar inda akasarin ‘yan Nijeriya suka lulluɓe cikin yanayi na firgici da damuwa. A baya-bayan nan ne dai rundunar sojin Nijeriya ta rashin kimanin mutane 37 da suka haɗa da Manjo da kyaftin da wasu muƙaman soji a wani harin kwantan ɓauna da suka kai a Jihar Neja. Kamar yadda abin baƙin ciki ya kasance, ya ƙara da cewa adadin mutanen da aka kashe a Nijeriya ya ƙaru kowace shekara da kashi 47 zuwa 10,366 a shekarar 2021, a cewar bayanan da SBM Intelligence ta tattara.

Abin baƙin ciki, a ra’ayinmu, an ce an kashe ’yan Nijeriya 1,743 a rubu’in farko na shekarar 2022, inda Neja da Zamfara ke kan gaba a da waɗanan adadi da ɗangaren bayanai da bincike na kafafen yaɗa labarai suka fitar kuma suka tantance. Abin takaici ne a ra’ayinmu cewa duk da irin ƙoƙarin da jami’an tsaro suke yi, ta’addanci, ’yan fashi, tada ƙayar baya, damfara ta intanet, manyan laifukan da suka shafi ƙasashen duniya, da kuma rikice-rikicen ƙabilanci sun ci gaba da haifar da ƙalubale ga tsaron ƙasa.

Ba za a iya ƙayyade tasirin hakan ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya ba duk da cewa ana ci gaba da korar mutane daga yankunansu. Ya zuwa watan Disambar 2021, adadin ’yan gudun hijira a Nijeriya ya qaru daga miliyan 2.1 a shekarar 2018 zuwa miliyan 2.9, in ji shafukan yanar gizo na UNHCR.

A matsayinmu na jarida, mun san cewa idan babu tsaro, ba za a samu jari ba, kuma idan ba a zuba jari ba, ba za a samu cigaban tattalin arziki ba, sannan kuma samar da abinci zai zo da ƙalubale, kasancewar manoma ba za su iya zuwa gonakinsu ba. Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana a fili lokacin da ya gane cewa ƙarfin soja kaɗai ba zai iya tabbatar da ɗorewar tsaro da kwanciyar hankali ba.

A ra’ayinmu, ba za a iya daƙile ƙalubalen ba idan har babu kayan aiki, wanda hakan zai iya jefa tambayar ta yaya za mu iya tabbatar da aikin ’yan sandan ƙasar nan? A lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, an bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe ƙarin dala biliyan 1 a kasafin kuɗi tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023, wajen magance matsalar rashin tsaro.

Ba tare da kyara ba game da shirin inganta tsaro, muna da ra’ayin cewa akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan da suka dace da ɓangarori daban-daban domin tinkarar matsalolin tsaro yadda ya kamata.

Wani muhimmin abu, a ra’ayinmu, shine buƙatar gwamnati ta duba hanyoyin samar da ingantacciyar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro daban-daban don inganta haɗin gwiwa don samar da haɗin kai a ƙoƙarin yaƙi da rashin tsaro.

Muna da ra’ayin cewa dole ne a sabunta sojojin mu da kuma ƙarfafa su ta hanyar saka hannun jari a cikin manyan maƙamai, damar tattara bayanan sirri, tsarin sa ido, da kayayyakin kariya.

Za mu iya ganin gagarumin ci gaba ne kawai idan akwai himma da isassun ma’aikata, kuma idan za mu iya tura fasaha a cikin yaƙi da miyagun laifuka, da jirage marasa matuƙa a daidaitattun wurare da wuraren ‘yan bindiga.

A halin da ake ciki na tsaro a ƙasar nan, ya zama dole mu tavo ayar tambayoyi dangane da yadda ake tallar na’urori na CCTV a manyan birane. Mene ne ya faru da babbar kyamarar sa ido ta fasaha tare da Sat 1 da Sat 2 a cikin orbit ɗin mu, da gaske, ya kamata mu dubi abin da za mu iya yi daban-daban a matsayinmu na al’umma wanda zai ba mu sakamako mai kyau wajen ganin cewa mun magance matsalolin da ke haifar da rikice-rikice, inganta haɗin gwiwar zamantakewa, da bunƙasa tattalin arziki.

Wannan, a ra’ayinmu, yana buƙatar zuba jari mai tsoka a fannin ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi, da samar da ababen more rayuwa da za su baiwa ƙasar damar samar da wani yanayi da tsattsauran ra’ayi ba zai samu wani wurin zama ba.

Dangane da haka, akwai gaggawar haɗa kai da ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa don aiwatar da shirye-shiryen da za su magance bambance-bambancen zamantakewar al’umma da ke haifar da rikice-rikice da kuma buqatar masu ruwa da tsaki da suka haɗa da kamfanoni masu zaman kansu, ƙungiyoyin farar hula, da kuma al’ummomin yankuna.

Mun gane cewa aikin kare ƙasa ba ya kan wuyan jami’an tsaro ko gwamnati kaɗai. Haƙiƙa, nauyi ne na gama kai wanda ke buƙatar sa hannun kowane ɗan ƙasa. A kan haka ne muke kira ga ’yan Nijeriya da su sa ido sosai, su kai rahoto ga hukumomin da suka dace, da kuma tallafa wa rundunar soji a aikinsu na kare ƙasa.