Abin da ya sa ‘yan sandan Nijeriya ke shan wahala – Majalisar Dattijai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattijan Nijeriya ta ce halin da aikin ‘yan sanda ke ciki a kasar na buƙatar a zauna a sake masa fasali.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mataimakin shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya ce ba a gina hukumar ‘yan sandan Nijeriyar kan yadda za ta yi nasara ba.

Sanata Ahmed Abdulhamid Malam-Madori wanda shi ne shugaban kwamitin aikin ‘yan sanda na Majalisar dattijan ƙasar, ya shaida wa BBC cewa tabbas batun haka yake, saboda yadda ake da ƙwararrun ‘yansanda a ƙasar da za su iya fitar da ita a idon duniya, sai dai aikinsu na cikin gida babu inganci.

”Mu na da ƙwararrun ‘yan sanda da suka goge a fannin aiki, kuma ko ina muka shiga da su ba za mu ji kunya ba, amma ƙarancin samun kuɗi na gudanarwa da rashin kyautata wuraren ba su horo da lalacewar makarantun ‘yansanda sun lalace idan aka kwatanta da na baya.

Sanata Ahmed Malam-Madori ya ce dole a kyautata wuraren da ake bai wa ‘yansanda horo, a kuma haɓɓaka aikin ‘yan sanda ta hanyar ƙara musu kuɗaɗe wajen kasafin kuɗi, da inganta wuraren horonsu da duk wani abu na kyautatawa gare su.

Ya ƙara da cewa “yadda ake gudanar da kasafin kuɗi ta ɓangaren ‘yansanda abin bai taka kara ya karya ba, hatta a kasafin kudin bana ba a bai wa wurin fifiko ba,Inda ya ce ya kamata yadda ake bai wa sojin sama da na ƙasa da na ruwa kuɗi su ma ‘yansanda indai ba a ba su sama da na sojoji ba, to bai kamata a ba su ƙasa da haka ba, saboda idan ana batun tsaro ‘yansanda ne a sahun gaba domin sojoji ba wannan horon aka ba su ba.”

Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya ce akwai ƙudurori kan batun inganta aikin ‘yansanda da ‘yan majalisa za su gabatar a zauren majalisar, za kuma su yi ƙokarin ganin an tabbatar da su.

”A ciki akwai batun gyaran makantun ‘yansanda da suka lalace, akwai batun fansho saboda ‘yansanda na karbar mafi ƙanƙantar fansho, saboda abin da ake bai wa sojoji ya ninka wanda ake bai wa ‘yansanda, lamarin akwai tausayawa a ciki.”

An jima ana sukar gwamnatin Nijeriya kan batun na inganta aikin ‘yansanda, da albashi mai tsoka da muhalli da walwalarsu, abin da ake ganin na taka rawa wajen ta’azzara cin hanci da rashawar da ake zargin wasu ‘yan sanda da aikatawa. 

By ukarofi