Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Hukumar Kwastom ta Nijeriya, Bashir Adeniyi Adewali ya ce kimar makamai da miyagun ƙwayoyi da suka kama a rana guda a Jihar Ribas ya kai Naira biliyan 13.9.
Bashir Adewali ya bayyana cewa makaman biliyan N4.171 suka kama a Tashar Jiragen Ruwa ta Onne da ke Jihar Ribas a ranar Litinin.
Makaman a cewarsa sun haɗa da bibdigo guda 844 da kuma harsasai masu rai guda 12,500, waɗanda aka ɓoye suba cikin kayan daki da aka shigo da su daga ƙasar Turkiyya.
A tashar jiragen ruwan ne kuma jami’an hukumar kwastom suka kama kwantainoni guda shida ɗauke da kwalabe miliyan daya na maganin tari mai ɗauke da sinadarin Kofin.
Sauran ƙwayoyin sun haɗa da ƙwayar Tramadol guda miliyan 3.5, wanda jimillar kuɗinsu ya kai Naira biliyan 9.6.
Baya ga su, an kama wasu kwantainoni biyu dauke da kayan gwanjo da kuɗinsu ya kai miliyan N144.
Shugaban hukumar ya ce mai kayan fasa-ƙwaurin ya yi yunƙurin zille wa bincike domin tantance kayan a tashar jiragen ruwan amma dubunsa ta cika.
Ya ce za a miƙa makaman ga hukumar yaƙi da ƙananan makamai da ke ƙarƙashin Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, domin gurfanar da mutane uku da aka kama kan zargin alaƙarsu da makaman.
