Abin kunya a Nijeriya (II)

Spread the love

Ci gaba daga makon jiya.

Shin gwamnatin Nijeriya ba ta san wannan ba ne? Abinda ake yi na kashe mutanen karkara a yankunan Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna, Neja da Kebbi ba dainawa aka yi ba. Muna da dakarun da za su iya yin yaƙi a kowacce ƙasa don kwantar da tarzoma, amma abin mamaki sun kasa kawo ƙarshen wasu tsirarun mutane da suka ɗauki makami suna ta’addanci. Kullum sai maganganun banza a kafafen yaɗa labarai da jaridu gami da gidajen Talabijin kan cewa ana cin galaba a kan ‘yan bindiga, an sayo jiragen yaƙi, an sayo makamai. Amma har yanzu mutanen karkara a inda ‘yan bindiga suke musguna musu ba su daina fuskantar ƙalubalen ‘yan bindigar ba.

Wani ƙarin abin kunyar da cin amanar ƙasa da manyan ƙasar nan suka yi (musamman ‘yan Arewa) shi ne yadda suka karɓi maƙudan kuɗaɗe a hannun Tinubu suka mara masa baya a kan sun amince ya zamo shugaban ƙasa, duk da suna sane da cewa ba shi da wani tanadi na musamman kuma mai muhimmanci ga ƙasa da kuma Arewacin ƙasa, amma suka mara masa baya. Shi kansa an tambaye shi me zai yi wa Arewa (musamman a kan matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa?) a nan ma bai ce ya tanadi wani abu ba. Amma duk da sanin haka manyan Arewa suka mara masa baya yanzu yake mulkarmu.

Kullum rayuwa ƙara munanta take, talaka yana ƙara faɗawa masifar rayuwa, a yayin da su kuma sun killace iyalansu suna rayuwar farin ciki da jin daɗi. A Nijeriya ne mutum zai riƙe muƙamin Ministan gona, ko ministan lafiya, ilimi, tsaro ko sufuri. Ko kuma ya riƙe Kwamishinan ruwa ko na ƙananan hukumomi a jiharsa na shekara huɗu kacal, amma sai ka same shi da manya-manyan kadarori irin su; otel-otel, gidajen mai, rijiyar mai, danƙara-danƙaran gidaje gari guda a ƙasar Dubai ko manya-manyan gonaki a ƙasar Turawa, ko wasu kamfanoni da sauransu.

Wannan sace-sacen kuɗin da ‘yan siyasa da masu riƙe da madafun iko suke yi, tun daga kan kansila har zuwa shugaban ƙasa, ba komai suke yi ba face abin kunya da tozarta ƙasarmu Nijeriya a idon sauran ƙasashen da tuntuni sun kakkaɓe cin hanci da rashawa.

Ina da yaƙini a kan cewa, talakan Nijeriya ba shi da wani burin da ya wuce yin rayuwarsa ta rufin asiri a cikin salama. Ya samu abin yi, ya fita kasuwa yayi sana’arsa cikin kwanciyar hankali, ya saye da sauƙi ya sayar da sauƙi, yaje duk inda yake so cikin sauƙi. 

A lokacin mulkin marigayi General Sani Abacha an ce ya saci kuɗi ya kai ƙasar Ingila ya ɓoye, amma abin mamaki har yanzu akwai wanda idan aka bashi labarin sai ya ce bai san ma an yi ba, kuma yana raye da wayonsa a lokacin mulkin Abachan. To amma me ya kawo har bai sani ba? Saboda a lokacin akwai adalci a cikin mulkin, kowanne talakan ƙasa yafi ƙarfin abinda zai ci, da abinda zai sha, da suttura, muhalli da sauransu. To amma yanzu fa? Talaka baya cin moriyar dimokraɗiyyar siyasa, amma kuma ta ko’ina danne shi ake, hatta da shure-shuren mutuwar da yake yi an ƙi bari ya samu sassauci ƙara turmushe shi ake yi.

Don haka ya rage naku ku gyara ko kar ku gyara, dukkanninmu dai zamu mutu mu koma ga Allah, kuma tabbas! Wallahi tallahi sai an yi mana hisabi tsakaninmu da ku. Kowanne shugaba da ya jagoranci al’umma na kwana ɗaya kacal ba ma watanni ko shekaru ba, za a zo dashi ɗaure cikin sarƙa a gaban Allah da mutanen da ya mulka, adalcin da yayi wa wannan al’ummar shi zai kwance shi. 

Nafi’u Salisu

Daga NAFI’U SALISU.

Marubuci/manazarci. Ya rubuto daga Kano Nijeriya. [email protected]@gmail.com. 09056507471-08038981211.

By ukarofi