Taron ‘Nijeriya Week’: Yadda Abdulkareem Muhammad ya samu kyautukan karramawa har guda uku

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A ƙarshen watan Yulin da ya gabata ne aka gudanar da taron karrama finafinai ta duniya  da ake gudanarwa  duk shekara mai taken “Nijeriya Week” a birnin Landan na ƙasar Ingila wanda ya samu halartar masu harkar fim daga ƙasashe daban daban na duniya.

Abdulkareem Muhammad wanda jigo ne a masana’amtar finafinai ta Nijeriya, yana ɗaya daga cikin manyan baƙi da suka halarci taron, kuma baya da kasancewar sa babban baƙo ya shigar da fim ɗin sa mai suna ‘Kuka Bulukiya’ wanda kamfanin sa Moɓing Image Limited ya shirya, kuma fim ɗin ya kasance shi ne ya ci gasa mafi girma. Haƙiƙa shi ma Abdulkareem Muhammad ya samu karramawa ta musamman, kuma kamfanin sa na Moɓing Image, shi ma ya samu karramawa a matsayin mai bayar da gudunmawa a kan harkar fim da yake gudanar da taron bajekolin finafinai na Afirika a duk shekara, wato Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festiɓal. 

Bayan dawowar Abdulkareem Muhammad gida daga Birnin Landan wakilinmu ya tattauna da shi domin jin yadda taron ya gudana da kuma karramawar da ya samu da kamfaninsa da kuma fim ɗin da ya shirya.

Inda ya fara amsa tambayar mu da cewa;

” To  abin da ya faru akwai wani taro da ake shiryawa a birnin Landan da ake kira ‘Nigerian Week’ Wanda ake ware sati domin a nuna ayyuka da ake yi na Najeriya. A harkar saka kaya ne, da kaɗe -kaɗe da finafinai, abinci da al’adun Nijeriya. Shi ne ake yin wannan ‘Nigeria Week’ ɗin a birnin Landan. To a cikin wannan abu da ake yi, sai kuma aka ɓullo da gasa wadda idan ka na da fim za ka iya shigar da shi, a duba shi a ma’aunin da ya cancanta a bayar. 

To Alhamdulillah, kamfanina na Moɓing Image Limited, ko da yake an gayyace ni dama can kafin wannan biki za su karrama ni da kyautar Zakakurin mai aiki a rayuwa. To a kan wannan ne dai aka kira ni na je birnin Landan, a ranar 28 ga Yulin da ya gabata wanda a ranar ne aka yi bikin.

Kuma daman kafin lokacin na tura musu cewa muna da buƙatar mu shiga gasar ta finafinai da ake yi, don haka muka tura da fim ɗin mu mai suna ‘Kuka Bulukiya’ ya shiga wannan gasar. Kuma sakamakon gasar da muka shigar, na farko dai wannan fim na ‘Kuka Bulukiya’ ya zama zakaran gwajin dafi, don shi ne ya fito a fim ɗin da ya fi kayatarwa a wannan gasa da aka yi. Sannan kuma aka duba a ma’auni aka ga irin ayyukan da Kamfanin Moɓing Image Limited suke yi da kuma wannan fim ɗin na ‘Kuka Bulukiya’, sai aka ga cewa  Kamfanin Moɓing Image Limited suna taka rawa wajen bunƙasa abubuwan da suke harka ta finafinan Nahiyar Afirika. Saboda kada ka manta cewa Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festiɓal, da ake yi a kowacce shekara, shekaru shida da suka gabata, ya shiga ma’aunin da a duniya ma suna ganin, wannan abu da ake yi ya zama wata matattara da tattaro mutanen da suke koyar  da harkar daga jami’o’i kuma su zo su koyar da harkar ta hanyar gabatar da muƙaloli. Bayan sun gabatar kuma a fito da littafi  a kan taken da aka ɗauka a kowacce shekara. To wannan abu ya shiga cikin tsarin yadda aka kalli Kamfanin Moɓing Image Limited cewa muna taka rawa wajen bunƙasa harkar fim. Sannan kuma ga gasa da ake yi na cewa duk harsunan da suke na Nahiyar Afirika za su shiga wannan gasar, kuma a fito da kyaututtuka har goma sha shida, kuma a bai wa mutane. Sannan kuma muna zaɓar zakakuran mutane mu ce mun ba su kyautar zakakuran mutane mu ba su kyautar waɗanda suka yi aikin na hudimtawa jama’a a rayuwa.

Duk waɗannan abubuwan an duba aka ga cewa Kamfanin Moɓing Image Limited ya na taka rawa a harkar bunƙasa yanayin da ake yin finafinai a Afirika. Wannan ta sa aka ba mu wannan karramawa a matsayin kamfanin da ya yi fice a wannan shekarar.”

Da muka tambaye shi ko ya ya kalli irin wannan nasarar da ya samu kuwa cewa ya yi,

“To Alhamdulillah! Wannan ta fita daman, saboda sai ma aka fitar da matsayin ba ma wai Kano ba. Ba ma Nijeriya kawai ba an kai ga wata ƙasa ne a Turai wato Ingila, a birnin Landan, aka ce shi mutane sun fito daga wannan ƙasa, ko’ina na sashin ƙssar nan, kuma aka ce an ba ka wannan kyauta, to wannan ba ƙaramin abu ba ne ba.

Na biyu kuma, mahangar da aka saka Kamfanin Moɓing Image Limited da abin da muke yi na KILAF AWARD dinnan, har ya kai cewa Tubaran su ya kallo sun ga cewar abin da ake yi dinnan ya cancanta a yaba masa, kuma aka ya ba ɗin, to ka ga abu ne da gaskiya ya faranta mana rai, kuma muna yi wa Allah godiya da ya ba mu wannan ci gaba a wannan harka da muke ciki. Kuma gaskiya ba ƙaramin ƙarfin gwiwa muka samu ba, saboda mun ga yadda aka yi ma’am da mu a wannan waje, kuma mun ga yadda aka yaɗa abubuwan da muka yi cewa gaskiya mun taka rawa, ko kuma muna taka rawa mai kyau, dole mutum ya kasance ya zama cewa an burge shi, kuma an ɗan ƙarfafa shi a kan ya ƙara ƙaimi ya kuma zage damtse don ya ci gaba da bada ta sa gudunmawa kamar yadda aka saba.

Don haka ina rufewa da godiya ga Allah da damar da ya ba mu muke taka rawa daidai iya yadda muka iya yi, kuma har wasu su kalla su ga cewar sun yaba da abin da ake yi.”

By ukarofi