Ranar Hausa: Yunƙurin Hausantar da kimiyya da fasaha 

Spread the love

Daga FARFESA FARUK SARKINFADA

Haƙiƙa ilimin kimiyya da fasaha baiwa ce ta Ubangiji Ya keɓanci wasu daga cikin bayinsa da ita, wanda su kuma suke da haƙƙin sanar da wanda Ubangiji ya so. Amma kuma amfaninsa da tasirinsa da yin aiki da shi ya shafi kowa da komai. Don haka ba sai mutum ya karanci ilimin kimiyya da fasaha a makaranta ya cancanta ya san shi ko ya yi aiki da shi ba. Ma fi sauƙin sanar da ilimin kimiyya da fasaha ga al’umma shi ne samar da shi da koyar da shi cikin yarensu, ta yadda zai yi sauƙin fahimta gare su da kuma al’umma masu zuwa bayansu. Wannan zai kau da ƙalubalen gwagwarmayar koyon harshe Turanci ko Faransanci da sauran harsunan da ke ɗauke da wannan ilimi na kimiyya da fasaha kafin saninsa. 

A wani ɓangare kuma, samar da ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa zai taimaka wajen haɓaka ci gaban al’umma da ƙasa bakiɗaya kamar yadda ya tabbata a sauran ƙasashen da suka ci gaba kamar su Chana da Germany, ta hanyar koyar da ilimin kimiyya da fasaha a harshen uwa da suke yi a ƙasashensu. 

A Nijeriya, tuni  a na ta yunƙurin samar da ilimin kimiyya da fasaha a harshen Hausa ta fannoni daban-daban tare da kiraye-kirayen samar da dokar da za ta bayar da damar koyar da darussan Kimiyya da fasaha cikin harsunan ƙasa a Nijeriya a matakin gwamnatin tarayya da jihohi. Haƙiƙa zai fi sauƙi a horar da malaman da za su koyar da yara ilimin kimiyya da fasaha cikin Hausa fiye da koya wa dalibai harshen Turanci sannan su koyi wannan ilimi. 

Haƙiƙa harshen Hausa yana da nagarta da bunƙasa a nahiyar Afrika da wasu sassa na duniya, ta yadda za a iya samar da dukkan fannonin ilimi a cikinsa, duba da yadda ya shahara a duniya wajen yin amfani da shi a kafafun yaɗa labarai masu yawa a faɗin duniya. Bugu da ƙari Allah ya albarkaci al’ummar Hausawa da ƙwararru a dukkan ɓangarori na ilimin kimiyya da fasaha ta yadda babu fannin ilimin da ba za a iya samar da shi cikin harsen Hausa ba a yanzu. Don haka ya zamo ƙalubale ga Hausawa masana ilimin kimiyya da fasaha su ƙara ba da himma a kan samar da wannan ilimi cikin harshen Hausa. 

A shekarun baya, masana da dama sun wallafa littattafai da ƙasidu a wasu fannonin kimiyya da fasaha a cikin harshen Hausa. Misali, Malam Abubakar Imam da wani Bature mai suna Rupert East sun wallafa littafin ‘Ikon Allah’ mai ɗauke da labaran halittu iri-iri na duniya. Farfesa Hambali Junju ya rubuta littafin ‘Garkuwar Hausa da Tafarkin Ci gaba’ mai ɗauke da fassarar wasu kalmomi da suka shafi kimiyya da fasaha cikin Hausa. Farfesa Muhammad Kabir ya rubuta littafin ‘Aikin Likita’, yayin da marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa ya rubuta littafin ‘Kimiyyar Sararin Samaniya’. 

A wannan zamani kuma, Jami’o’in Nijeriya da na wajen Nijeriya sun fara samar da fassarar littattafan kimiyya da fasaha kamar Lissafi, Physics, Chemistry, Biology, Kimiyyar Computer cikin Hausa. A wani ɓangare kuma ɗaiɗaikin mutane su na rubuce-rubucen littattafa da ƙasidu, kai har da waƙoƙi da su ka shafi kimiyya da fasaha a cikin Hausa. Misali, na wallaf littafin ‘Wani Abu a Kan Matar Sarki’ a kan Ilimin ‘Yan Halittu, watau microbes, da littafin ‘Zaton Wuta a Maƙera’ a kan cutar yoyon fitsari da yadda za a magance aukuwarta. Na kuma wallafa tare da rera waƙoƙi a kan cimaka (nutrition) da cutar Korona a cikin Hausa. Har wa yau akwai wasu masana da su ke koyar da darussan Kimiyya da Fasaha a shafukan sada zumunta na Facebook da YouTube da dai sauransu. Akwai kuma cibiya mai zaman kanta ta Engausa Global Tech Hub da ta himmatu wajen koya wa matasa fasahar ƙere-ƙare da sana’o’i na zamani a cikin Hausa. 

To amma akwai buƙatar ƙara zaburar da masana su samarda ingantattun rubuce rubuce, musammam littattafa da sauran kayayyakin koyo da koyarwa cikin harshen Hausa, waɗanda su ne muhimman kayan aikin ɗabbaka dokar koyar da darussan kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa. 

Tuni mun assasa wata Gidauniyar Bunƙasa Kimiyya da Fasaha cikin Hausa mai zaman kanta da manufofi kamar haka:

1. Gamayyar ƙwararru a fagen kimiyya da fasaha da kuma masana harshen Hausa don samar da ingantaccen ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa, don ƙarin yaɗuwarsa da tasirinsa ga ci gaban al’umma. 

2. Alaƙanta al’adu da fasahar Hausawa da kimiyya da fasahar zamani, don bunƙasa tasirinsu ga ci gaban al’umma.

3. Wallafa ƙasidu da mujallu da muhimman labarai da suka shafi ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa domin ilmintarwa da wayar da kan al’umma bisa abubuwan da suka shafi kimiyya da fasahar zamani. 

4. Bada gudunmawa da samar da manhajoji na koyo da koyarwa da bincike kan fannoni daban-daban na kimiyya da fasaha a cikin harshen Hausa, domin samar da ƙwararrun masana kimiyya daga tushe a al’ummar Hausawa. 

5. Amfani da kafafen sadarwa na zamani, don tabbatar da tsarin koyo da koyar a kimiyya da fasaha cikin al’ummar Hausawa. 

6. Samar da mahanga / shawarwari don nusarwa ga mahukunta da masu ruwa da tsaki a kan kafa dokoki da ƙudure-ƙudure bisa aiwatar da ilimin kimiyya da fasaha a harshen Hausa a dukkan matakan ilimi.   

A yayin da masana cikin jami’o’i da sauran manyan makarantu su ke aikin samar da ilimin kimiyya da fasaha cikin Hausa, wannan cibiya za ta zamanto magama mai tattaro dukkan masu ruwa da tsaki kamar gwamnati, masarautu, shuwagabannin addini, mawadata, ƙungiyoyin marubuta da bunƙasa al’adu, ‘yan jarida, ƙungiyoyin ci gaban al’umma da dai sauransu, wajen samarwa da yaɗa ingantaccen ilimin Kimiyya da Fasaha da kuma amfaninsa ga ci gaban al’umma. 

Abin tambaya da jan hankali a nan shi ne, yaushe za a fara koyar da ɗalibai ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa a ƙasar Hausa? Ta ina za a fara? Kuma waye zai fara? Idan ba mu taka rawar kiɗan mu ba, to fa wasu za su taka mana. 

Allah ya yi mana jagora. 

By ukarofi