Abin takaici ne yadda wasu alaramomi ke harkokin addini, inji Sarkin Misau 

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Mai Martaba Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Suleiman, ya bayyana takaicinsa bisa yadda ake kiran malamin tsangawa ko Islamiyya da alaramma, amma idan aka yi bibiyar iliminsa, sai a iske bai ma iya gudanar da ayyukansa na ibada da aka halatta masa, domin gudanar da su ba.

Sarkin ya ce, “Abu ne na ban takaici matuƙa gaya, ka ga mutum ana ce da shi Alaramma, amma sai a iske yadda yake yin alwala ma akwai gyara ko kura-kurai a ciki, lamarin da ya kasance koma-baya wa sahihin ibadojin mutum da rayuwar sa.”

Sarkin na Misau sai ya bayyana cewar, “Wasu sun riji’a akan cewar, haddace Alƙur’ani Maigirma ba tare da ilmantuwa da fassarar sa ba, ko karanta shi da lafazin da ya dace ba, ba abune na damuwa ko wajibi ba.

Alhaji Ahmed Suleiman, wanda ya ke tofa albarkacin bakinsa wa taron bita na kwanaki biyu wa malaman tsangaya da Islamiyya da aka zaƙulo mahalarta daga sassa daban-daban na jihar Bauchi, wanda kuma aka kammala shekaran-jiya Laraba a garin Bauchi, ya ce ire-iren wannan bita ce za ta fahimtar da malamai da almajirai dukkan lamura da suka jivanci aiwatar da ayyukan addinin Musulunci ko yin bauta wa Mahalicci, yadda ya dace.

Tunda da farko a cikin ƙasidar taron da ya gabatar mai taken “Farfaɗo Da Inganta Ilimin Tsangaya Da na Islamiyya a Jihar Bauchi”, Shehin Malami Ibrahim Ahmed Maƙari ya bayyana cewar,  Alqur’ani Maigirma shi ne littafi wanda yake yin jagorancin rayuwar ɗan-adam, ko ɗaukacin halitta baki ɗaya dake kan doron ƙasa.

“Allah Ubangijin dukkan halittu shine ya samar da wannan littafi Alƙur’ani (Manual kamar yadda nasara ya kira) domin ɗan adam ya riƙa komawa ga wannan Kundi da zummar sanin yadda zai gudanar da tsarin rayuwa, kuma da yadda zai sadu da Mahaliccin sa kan sahihiyar turbar lafiya, da yadda zai bi Ubangiji ta yadda Allah yake so, kamar yadda kundin Alkur’ani ya shimfida”.

Farfesa ko Shehin Malami Ibrahim Maƙari, wanda shine shugaban cibiyar ‘Bincike Kan Wanzar da Zaman Lafiya Da Lalubo Hanyoyin Cigaban Al’umma’ (Centre for Peace Research and Development), shine kuma jagoran wanda bita da Ofishin Uwargidan Gwamnan Bauchi, A’isha Bala Abdulkarim Mohammed na Gidauniyar Al-Muhibbah ta shirya, tare da haɗin kan Cibiyar Shehin Malamin.

Shehi Ibrahim ya ce, “Maƙasudin shirya irin wannan bita ta Malaman Ilimin Alƙur’ani da sauran wasu fannonin ilimi da suka jiɓanci addinin Musulunci shine, la’akari da cewa babu wani fannin karantarwa da’a yau yake fuskantar rashin kula da wofintarwa daga ‘ya’yan sa (Musulmi) kamar  Alƙur’ani Maigirma. Kuma bisa son kula da littafin da koyarwar sane ya kawo bukatar a riqa gudanar da ire-iren wannan bita domin fahimtar koyarwar addinin Musulumci”.

“Shi Bature, biyo bayan ganewar sa na muhimmancin koyar da karatun ilimin Alƙur’ani ne ya sa yake yin iyakar iyawar sa na ganin yadda zai hana karatun ilimin Alƙur’ani yin wani katavus a tsakanin al’ummar Musulmi. Farkon abinda Bature ya bijiro shine, ya ce ‘Ma’abuta makarantun tsangaya dukkan ilimin su, dukkan karatun su, dukkan abinda ma’abuta ilimin Alqur’ani za su yi na karatu, tunda ta hannun dama suke karatu, sunayen su jahilai (illiterates).

Imam Ibrahim ya cigaba da kawo manufar Bature na cewar, “Idan ma za’a ɗauki ma’abuta ilimin Alƙur’ani, a ba su aiki na hukuma mai sakamakon albashi, babu kowane irin taimako da idan mutum ya karanta wancan fanni na ilimin Alƙur’ani, idan ma za a ɗauke shi aikin hukuma na albashi, sai dai a dauke shi kawai ya zama Ana-Khallahu a makarantar firamare, ko ya zama Mukhti a kotun shari’a, ba zai wuce nan ba.”