Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Katsina ta bayyana cewar ta samu nasarar hallaka wani ƙasurgumin varawon daji mai suna Nazifi Ibrahim.
Rundunar ta kuma ƙwato tarin alburusai da wasu makamai a yayin fafatawa da ta wakana tsakanin su da wata tawagar masu garkuwa da mutane, a Ƙaramar Hukumar Faskari dake jihar ta Katsina.
Kakakin rundunar, ASP Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar game da yaƙi da ‘yan ta’addan daji a jihar.
A cewar sanarwar, a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 rundunar ta samu bayanai da ke nuni da cewar wasu ‘yan fashin daji ɗauke da manyan bindigogi sun afka wa qauyen ‘Yankara dake cikin ƙaramar hukumar Faskari, inda ba da jimawa ba babban jami’in ‘yan sanda na ƙaramar hukumar ya jagoranci tawagar ‘yan sanda, ‘yan banga da kuma rundunar tsaro da gwamnatin jihar ta kafa zuwa ƙauyen.
Ko da varayin su ka lura da jami’an tsaron sai suka buɗe ma su wuta, inda bayan musayar wuta tsakanin bangarorin biyu rundunar ta samu nasarar hallaka jagoransu Nazifi Ibrahim mai shekara 22, a yayin da sauran varayin su ka tsere cikin daji.
“Bisa ga bayanan da rundunar ta samu, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ɗauke da muggan makamai irin su AK 47, sun kai farmaki wata gona da ke bayan ƙauyen ‘Yankara.” Inji sanarwar.
ASP Aliyu ya ce tawagar jami’an tsaro ta kuma ƙwato ragayar alburushi guda 185 mai tsawon 7.2mm da ku ma harsashin bindigar AK 47 guda 90 da wasu makamai da aka ɓoye cikin buhu.
Daga ƙarshe sanarwar ta buƙaci shugabannin jami’an tsaro dake ƙananan hukumomin jihar, da su ƙara zage damtse wajen samar da sabbin hanyoyi, gami da yin haɗin guiwa da sauran jami’an tsaro, wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
