Abinda ya sa na umarci a cire tozuna a manyan titina – Ministan Ayyuka

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Ayyuka, David Umahi ya ce ya umarci a cire tozuna a manyan titinan Nijeriya ne don inganta zirga-zirgar ababen hawa da rage cinkoso a titinan.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani zama na kwana biyu da injiniyoyi da manyan ma’aikata a Abuja, ranar Juma’a.

Zaman, wanda Ma’aikatar ta shirya, an yi masa take ne da; ‘Ensuring Delivery Mr. President’s Agenda on Road Infrastructural Development’, wato tabbatar da isar da ayyukan Shugaban ƙasa game da bunƙasa ci-gaban titina.

Ya ce yana da muhimmanci a cire tozunan sakamakon haifar da haɗurra da suke yi da tsawaita lokacin tafiye-tafiye, ya na mai bada misali da wata tafiyar sa’a guda da ya yi acikin sa’o’i uku sakamakon sanya tozo a dukkanin tsawon mita 20 ta hanyar da ya bi.

Ya kuma ce akwai wuraren da suke buƙatar a sanya tozuna wanda a halin yanzu abinda suke ƙoƙarin yi kenan, ya na mai cewa majalisa ta umarci a cire tozunan rage gudu da aka sanya a wuraren da ba a buƙatarsu.

Ya ƙara da cewa sai an samar da tazarar mita 100 na gargaɗi ga masu ababan hawa a manyan titina domin su faɗaka.

Kazalika, ministan ya yi tsokaci game da ayyukan ababen more rayuwa da gwamnatin Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin samarwa al’umma inda ya ce hakan suna samuwa ne don inganta harkokin tattali da rayukan al’ummar Nijeriya.

Umahi ya ce ya na da muhimmanci a wayar da kan al’umma don su fahimci agendar Shugaba Tinubu ta sabonta ƙasar inda ya bada misali da ayyukan titina a sassanta.