Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shekaru 32 bayan soke zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ranar 12 ga Yuni, 1993, wanda ake fi kira da ‘June-12’, tsohon Shugaban Nijeriya, Janar Ibrahim Babangida, ya amince a karon farko cewa, Marigayi Alhaji Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola ne ya lashe zaɓen.
Yayin da ya ke jawabi a wurin bikin ƙaddamar da littafin da ya rubuta kan tarihin rayuwarsa mai taken “A Journey in Serɓice” a Abuja, Babban Birnin ƙasar, IBB, kamar yadda ake yi masa laƙabi, ya ce, idan da zai samu wata damar, da ya tabbatar da zaɓen.
Mawallafin littafin, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, ya ce, “mai basira” da kuma “Maradona” da ake yi wa Babangida laƙabi da su ya sa ya amsa tambayar ko Abiola ne ya ci zaɓen ranar 12 ga watan Yuni ko a’a a littafinsa.
“Ko da yake a rubuce na bayyana bayan zaɓen cewa Abiola bai ci zaɓen ba, idan aka yi la’akari da shi, da kuma nazartar duk wasu bayanai da ake da su, musamman cikakken sakamakon zaɓen da aka buga a cikin wannan littafi, ko shakka babu MKO Abiola ne ya lashe zaɓen da aka yi a ranar 12 ga watan Yuni,” Babangida ya ce a cikin littafin nasa.
“Bayan an yi nazari sosai kan ainihin alƙalumman da aka tattara daga rumfunan zaɓe 110 a faɗin ƙasar, ya nuna a fili cewa, ya cika manyan ƙa’idoji biyu na lashe zaɓen muƙamin Shugaban ƙasa – musamman ƙuri’u mafi rinjaye da yaɗuwa – inda ya samu ƙuri’u 8,128,720 akan ƙuri’u 5,848,247 na Marigayi Alhaji Bashir Tofa da kuma tabbatar da lashe ƙuri’u a jihohi 28 har da Abuja daga cikin jihohi 36 da Abuja.
A yayin jawabinsa, Babangida, wanda aka fi sani da IBB, ya shaida wa taron cewa, soke zaɓen yana da matuƙar muhimmanci ga ƙasa.
“Na yi nadamar rushe zaɓen June 12, na kuma ɗauki alhakin matakin – wanda aka ɗauka a zamanin mulkina, na kuma ɗauki hakan a matsayin kuskure,” inji shi.
Sai dai ya ce, yana farin ciki da yadda tsohon shugaban mulkin farar hula da ya gabata, Muhammadu Buhari, ya tabbatar da nasarar Abiola tare da karrama shi da babbar lambar yabo ta ƙasa, wato Grand Commander of the Federal Republic (GCFR), wadda ake ba shugabannin ƙasar.
Dawowar mulkin dimukraɗiyya a Nijeriya a shekarar 1999 ya biyo bayan wasu abubuwa da suka faru har da zubar da jini ne.
A shekarar 1993, Babangida, wanda ya karɓi mulki a shekarar 1985 ta hanyar juyin mulkin da aka yi wa Janar Muhammadu Buhari, ya goyi bayan miƙa mulki ga farar hula tare da zaɓen gudanar da Shugaban ƙasa na 1993. Daga baya ya soke zaɓen kuma ya yi murabus sakamakon zanga-zanga da tashe-tashen hankula da suka biyo baya.
