Abun da aka shuka shi za a girba!

Daga SAMINU HASSAN

Wani sakamakon bincike na jin ra’ayin alumma, da jaridar The Guardian ta Amurka ta wallafa a baya bayan nan, ya nuna yadda duk cikin Amurkawa biyar, ɗaya daga cikinsu ke ganin abu ne mai kyau, a cimma burin siyasa ta hanyar tarzoma. Ko shakka babu hakan abun tsoro ne, da tayar da hankali, ganin cewa wannan tunani ya yi hannun riga da ainihin tushen dimokaraɗiyya, wanda ya tanadi cimma duk wani buri ta maslaha da kwanciyar hankali.

Wani abun lura game da wannan bincike, shi ne yadda Amurkawa ke saurin yarda da farfagandar ’yan siyasa, wadda ke haifar da rashin yarda, da nuna kyama, da amincewa ɗaukar matakan tada zaune tsaye, yayin da suke son cimma wani buri na siyasa ko zamantakewa.

Ko da yake dai Bahaushe kan ce Barewa ba za ta yi gudu dan ta ya yi rarrafe ba. Duniya ta ga misalin irin wannan tunani tun daga kan jagororin Amurka, inda alal misali, a ranar 6 ga watan Janairun shekarar bara, ɗaruruwan magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Donald Trump, suka yi kutse cikin ginin majalissar dokokin ƙasar na Capitol, da nufin hana bayyana tsohon shugaban ƙasar a matsayin wanda ya sha kaye a babban zaɓen da ya gabata. Wanda hakan ya sabbaba rasuwar mutane 7 da jikkatar gwamman mutane. Masu bibiyar lamarin sun tabbatar da cewa shi kansa tsohon shugaba Trump, ya nuna wasu alamu na goyon bayan wancan kutse.

Masharhanta dai na ganin idan har wannan yanayi na yin watsi da tushen dimokaraɗiyya ya ci gaba da kamari a Amurka, mai yiwuwa ƙasar ta fuskanci manyan bore masu nasaba da siyasa a nan da ’yan shekaru masu zuwa.

Domin kauce wa hakan, wajibi ne jagororin ƙasar su yi karatun ta-nutsu, su yi hangen nesa wajen wayar da kan Amurkawa, game da illar dake tattare da ɗaukar doka a hannu, da kin amincewa da mabanbantan raayoyi, da nuna isa, waɗanda dukkaninsu munanan dabiu ne da ka iya haifarwa ƙasar da maras ido.

Uwa uba kuma, ya zama wajibi gwamnatin Amurka ta dawo daga rakiyar manufarta ta shiga sharo ba shanu, da nuna ƙarfin tuwo ga sauran ƙasashe, ko nuna kyama ga hanyoyin ci gaba da sauran ƙasashe suka zaɓa wa kan su, domin kuwa irin wannan tunani ne ke haifarwa ’yan ƙasar ta yanayi na kangarewa, da kin karɓar gaskiya!