Yar shekara 64 ta lashe zaɓen Shugabar Ƙasar Indiya

Daga BASHIR ISAH

Rohotanni daga Ƙasar Indiya sun ce, Droupadi Murmu ‘yar shekara 64 daga ƙabila mara rinjaye, ta lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar.

Bayanai sun nuna Droupadi ta lashe zaɓen ne a ranar Alhamis, 21 ga Yulin 2022 tare da goyon bayan jam’iyya mai mulki.

Wannan nasarar ta sa Droupadi zama mutum na farko da zai taɓa riƙe wannan muƙami daga al’ummar da ake nuna wa wariya a ƙasar.

Wani ɓangare na sakamakon da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar ya nuna Droupadi wadda ‘yar asalin ƙabilar Santhal ce, ta samu goyon bayan da yawan ‘yan jam’iyyar MP da ma ‘yan majalisa wanda hakan ya yi tasiri matuƙa wajen nasarar da ta samu.

An ce Firam Minista Narendra Modi mai daga jam’iyyar ‘Bharatiya Janata Party’ (BJP), shi ne ya zaɓe ta don samun wannan muƙami.