Shugaban Amurka, Joe Biden ya harbu da COVID-19

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Yanzu haka Shugaban Ƙasar Amurka, Joe Biden, na can a killace a Fadar White House bayan da gwaji ya nuna yana ɗauke da cutar Covid-19.

Wannan na faruwa ne duk da Shugaban ya karɓi cikakken rigakafin korona, amma duk da haka ya nuna wasu alamu a tattare da shi, kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa inji sakatariyar yaɗa labarai, Karine Jean-Pierre.

A wani saƙon Tiwita da ya wallafa, Shugaba Biden ya ce yana lafiya kuma yana ci gaba da gudanar aikinsa.

Sai dai kuma, mai ɗakinsa Jill Biden ta ce, an gwada ta an kuma gano ba ta ɗauke da ƙwayar cutar.

Bisa la’akari da dokokin Fadar White House, Shugaba Biden zai ci gaba da gudanar da aikinsa ne daga inda aka killace shi har zuwa lokacin da aka sake gwada shi aka ga ya rabu da cutar, sannan sai rika halartar tarurruka ta bidiyo.

By Editor