Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A Juma’ar da ta gabata ne dai wata Kotun Shari’ar Muslunci da ke zamanta a unguwar PRP a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Abubakar Ayuba, ɗan kimanin shekaru 20 da haihuwa da laifin yi wa wani Salisu Usaini mummunan rauni a hannu, har ta kai ga hannun ya ruɓe a ka yanke shi a asibiti.
Laifin, a cewar alƙalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya saɓa wa sashi na 159 na kundin dokar laifuka (Penal Code) ta Jihar Kano.
Shi ya sa alƙali Ahmad ya yanke wa mai laifin hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari da kuma biyan diyyar Naira Miliyan 52 da dubu 970 a cikin shekaru ga mai ƙarar.
Alqalin ya kuma umarci wanda a ke ƙara da ya biya Naira dubu 650 kuɗin magani da wanda ya shigar da ƙara ya yi tun daga farkon jin raunin har zuwa warkewarsa.
Tun da fari dai, a ranar 20 ga watan maris, 2022 aka zargi Abubakar da ɗaukar wata sharɓeɓiyar wuƙa ya kuma kaftawa matashi Salisu Usaini a hannunsa na dama, kuma dalilin wannan aika-aikar da Abubakar ɗin ya yi ne ya janyo likitoci suka tabbatar da cewar babu shakka sai dai a guntule hannun, saboda tuni hannun ya ruɓe.
Ko da likitoci suka cire hannun matashin, sai fa hannu ya cigaba da ruvewa har sai da hakan ya sanya aka sake yi masa aiki, daga ƙarshe kuma sai da aka guntile hannun gaba ɗaya tun daga allon kafaɗarsa.
Da aka kai mai laifin kotu, mai gabatar da ƙara, Aliyu Zainul Abideen ne ya karantawa matashin tuhumar da ake yi masa, tun kuma a wancan lokaci Abubakar ya amsa wannan zargi da ake yi masa.
Hakan ne ya sanya kotun ta umarci jami’an gidan gyaran hali da su ajiye shi har sai an ga yanayin halin da mara lafiyar yake ciki.
