Moussa Faki Mahamat: Hulɗar Afrika da Sin abin koyi ne

Daga CMG HAUSA

Shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar tarayyar ƙasashen Afrika ta AU, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana a jiya Laraba cewa, hulɗar dake tsakanin AU da ƙasashen Afrika da Sin abin koyi ne a wannan zamani.

A kuma jiya, Moussa Faki Mahamat ya karɓi takardar aiki na sabon shugaban tawagar Sin a ƙungiyar, kana jakada na musamman, a hedkwatar AU dake birnin Addis Ababan ƙasar Habasha, Hu Changchun.

Moussa Faki ya darajanta dadadden zumuncin dake tsakanin Afrika da Sin, da kuma ci gaban da ɓangarorin biyu suka samu a hadin kansu, yana mai jaddada cewa, huldar dake tsakanin AU da ƙasashen Afrika da Sin, abin koyi ne a wannan zamani. Ya ce, AU na fatan ƙara haɗa kai da Sin, don gaggauta tabbatar da taron Dakar na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da sakamakon hadin gwiwar shawarar “ziri ɗaya da hanya daya”, ta yadda za a ƙara amfanawa al’ummomin ɓangarorin biyu.

A nasa ɓangaren, Hu Changchun ya nuna cewa, AU tana taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar dunƙulewar nahiyar Afrika waje guda, da daidaita haɗin kan ƙasashen Afrika wajen tinkarar COVID-19, da kuma shiga tsakanin a kan batutuwan dake jawo hankalin ɓangarori daban-daban a yankin.

Ya ce, Sin na dora babban muhimmanci kan dangantakarta da AU, tana mai fatan zurfafa haɗin kai da ƙasashen Afrika bisa manyan tsare-tsare da amincewa da juna, ta yadda za a ingiza hulɗar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.

Fassarawar Amina Xu