Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban Jam’iyyar ADC a jihar Katsina Alhaji Musa Usman Wamba Funtua ya yi wannan magana yayin da yake mai da martani kan kalaman ɓatanci da aka tura wasu a Ɗanmusa da Yantumaki suka yi don ɓata sunan jagoran jam’iyyar adawa na ADC a jihar,Dr Mustapha Inuwa.
“Jam’iyyar ta kuma lashi takobin cewa a zaɓ,e na shekara 2027 mai zuwa ,kafin sha biyun rana ta tiƙa APC da ƙasa a jihar Katsina,”inji Wamba.
Shugaban jam’iyyar ya ce idan al’ummar Ɗanmusa da Yantumaki ba su gode wa Dr Mustapha Muhammad Inuwa ba, game da samar masu da aikin Dam ɗin da ya yi ba, bai kamata kuma su zage shi ba.
Wamba ya ce waɗanda suka yi waɗannan maganganun kamata ya yi su fara bincike, kafin furta wani abin da ba su san kan yadda yake ba
Alhaji Wamba ya ce wannan aikin da suke magana a kai, dan majalisar Jibia/Kaita Hon Sada Soki jibiya tun a wancan lokacin, saboda kyakkyawan dangatakar da Mustapha Inuwa wanda shi tsohon sakataren gwamnatin jihar ya kuma amince ya kawo shi a nan yankin Ɗanmusa da Yantumaki.
Shugaban jam’iyyar na ADC a jihar ya bayyana cewa aikin ba ma na wannan mazaɓar bane, amma wasu da aka turo don su ci wa jagoran na ADC mutucin, suka faɗin abin da ba su san kan yadda yake ba.
Wasu mazauna yankin Ɗanmusa da Yan tumaki a ƙaramar hukumar Ɗanmusa kuma mahaifar Mustapha Inuwa suka fito suna zargin shi madugun adawar da yin kwangilar aikin Dam da samar da ruwan sha a Ɗanmusa da Yan tumaki da har yanzu ba a kammala ba.
Zargin da Mustapha Inuwa ya musanta.
