Yanzu-yanzu: ASUU ta tsunduma yajin aikin gama-gari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya ASUU ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na makonni biyu a baki ɗaya jami’o’in da ke faɗin ƙasar.

Za a fara yajin aikin ne daga ƙarfe 12 na daren Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.

Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ya bayyana haka a Jami’ar Abuja yayin ganawa da manema labarai a yau Lahadi.

A cewarsa, hakan ya biyo bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 14 na gargaɗin da ƙungiyar ta bai wa Gwamnatin Tarayyar na ta warware matsalolin walwalar lakcarori da, samar da wadatattun kuɗaɗe ga jami’o’i da aiwatar da daɗaɗɗiyar yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta 2009.

Ya ce, baki ɗaya jami’o’in gwamnati za su kasance cikin yajin aikin, yarjejeniyar da aka cimma a zaman Majalisar Zartarwa ƙungiyar da ya gabata.

A ɓangaren Gwamnatin Tarayyar kuwa, ta ce an samu ci-gaba a tattaunawar da ke gudana tsakanin wakilanta da na ƙungiyar.

A ranar Larabar da ta gabata ne Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ya sanar da cewa gwamnati ta kai matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da wasu ƙungiyoyin manyan makarantu domin kauce wa samun tsaiko ga kalandar karatun ɗalibai.

By Babaji