CBN ya ba bankuna sa’o’i 48 su riƙa mayar wa kwastomomi kuɗaɗensu da suka maƙale a na’urar ATM

Spread the love

Babban Bankin NNijeriya CBN) ya umarci dukkan bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin kuɗi da su riƙa mayar wa abokan kwastomominsu kuɗaɗen da suka maƙale a sakamakon gazawar na’urar ATM cikin sa’o’i 48.

CBN ya yi haka ne domin kare masu amfani da bankuna da kuma dawo da amincewar jama’a ga tsarin kuɗi.

Umarni na ƙunshe ne cikin sabuwar ƙa’ida da Babban Bankin ya fitar mai taken ‘Jagororin Ayyukan Na’urar ATM a Najeriya’, wanda Daraktan Sashen Tsarin Biyan Kuɗi, Musa I. Jimoh, ya sanya wa hannu.

CBN ya ce bankuna su tabbatar da cewa idan sabis ya gaza, ana mayar da kuɗi nan take ko cikin awa 24 ga wanda ya yi hada-hada da bankinsa kai-tsaye, yayin da banki na daban kuma zai mayar da kuɗi cikin kwana biyu.

CBN ya kuma umarci bankunan da su inganta tsarin ATM ta hanyar saka kayan tsaro kamar kyamarori da kariya daga masu sata ta fasaha, tare da tabbatar da cewa na’urorin suna aiki ba tare da katsewa ba na fiye da sa’o’i 72 ba.

Hukumar ta ce, wannan gyara na daga cikin matakan da ake ɗauka don tabbatar da tsaron hada-hada da inganta tsarin biyan kuɗi a Nijeriya.

By Babaji