DAGA JOHN D. WADA a Lafia
Ɗan jaridar Daily Trust da ke wakiltar jaridar a Jihar Nasarawa, Kwamared Abubakar Abdullahi ya zama sabon shugaban masu turo da rahotanni wato Correspondents’ Chapel a turance na Ƙungiyar ƴan Jaridu ta (NUJ) reshen Jihar Nasarawa.
Kwamared Abubakar Abdullahi ne sabon shugaban, inda Christopher Nyamtu na gidan radiyon tarayya wato Federal Radio Corporation ya zama sakatare a zaɓen da aka gudanar. Wanda shugaban NUJ na jihar Kwamared Salihu Alkalib ya sa ido a kai.
Abdullahi ya lashe zaɓen ne bayan ya samu ƙuri’u 21, yayin da abokin takararsa, Danjuma Joseph na National Accord (jaridar yanar gizo) ya samu ƙuri’u 9.
Haka kuma, Christopher Nyamtu na Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN) ɗin ya lashe matsayin sakatare bayan ya samu ƙuri’u 21 inda ya doke abokin takararsa Augustine Kuza na jaridar Nigerian Pilot wanda ya samu ƙuri’u 9.
Sauran shugabannin da aka zaɓa sun haɗa da:
Kwamared Daniel Abel – Mataimakin Shugaba
Awayi Kuje (News Agency of Nigeria) – Mataimakin Sakatare
Michael David (Daily Independent) – Sakataren Kuɗi
Collins Agwam (Punch Newspaper) – Ma’ajin Kuɗi
Aliyu Muraki (FRCN Kaduna) – Mai Duba Lissafi (Auditor).
Shugaban NUJ na Jihar Nasarawa, Salihu Alƙali wanda ya gudanar da rantsarwa ya taya tsoffin shugabannin ƙungiyar murnar kammala wa’adinsu cikin nasara.
Alƙali ya bayyana tsohon shugaban, Isaac Ukpoju, a matsayin mutum mai gaskiya, amana, da tsantseni.
Ya kuma taya sabbin shugabannin ƙarƙashin jagorancin Kwamared Abubakar Abdullahi murnar nasarar da suka samu a zaɓen da aka kammala cikin gaskiya da lumana.
Yace “Zaɓen ya gudana cikin adalci da gaskiya, kuma ina yaba wa kowane ɓangare da ya taka rawa,” in ji Alƙali.
Ya shawarci sabbin shugabanni su gina bisa gado da jagoranci na baya, tare da tabbatar da cewa walwala da muradun mambobi sun samu muhimmanci.
Da yake jawabi bayan rantsarwa, sabon shugaban, Abubakar Abdullahi, ya yi alƙawarin aiki tuƙuru domin haɗin kai tsakanin mambobi da kuma kawo shirye-shiryen jin daɗin da zai amfane su baki ɗaya.
Ya gode wa kwamiti na zaɓe bisa gudanar da sahihin zaɓe mai gaskiya da amana, yana mai cewa:
“Jajircewarku da adalcinku ya ba mu ƙwarin gwiwa a tsarin.”
Abubakar ya kuma gode wa ƙungiyar NUJ ta jihar bisa lura da yadda aka gudanar da zaɓen cikin bin tsarin ƙungiya.
Ya ce bai ɗauki nasarar a matsayin cin nasara ko rashin nasara ba, sai dai a matsayin amanar hidima ga dukkan mambobi.
“Amanar da aka ba mu ita ce hidima ga dukkan mambobi, kuma ina ganin kowane memba ya zaɓe ni ne domin ci gaban ƙungiyarmu,” in ji shi.
Ya yi alkawarin jagoranci mai haɗin kai, wanda zai mutunta kowane memba da daraja da girmamawa.
“Zan yi aiki ba dare ba rana don tabbatar da haɗin kai tsakanin mambobi,” in ji shi.
Abdullahi ya kuma gode wa tsoffin shugabanni ƙarƙashin jagorancin Isaac Ukpoju, yana mai cewa:
“Jagorancinku ya kawo gagarumin ci gaba ga ƙungiyarmu, ba wai kawai za mu ci gaba da abin da kuka fara ba, za mu inganta shi.”
Sabon shugaban ya kuma yi alkawarin yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki don inganta sha’anin mambobi da kuma ƙarfafa ƙungiyar wajen cika manufofinta.
Tunfarko a jawabin sa, tsohon shugaban ƙungiyar wato Isaac Ukpoju wanda ya miƙa ragama ga sabbin shugabanni, ya bayyana wasu manyan nasarorin da suka samu a lokacin jagorancinsa, ciki har da samar da yanayi mai kyau na aiki da kuma kyakkyawar alaƙa da gwamnati.
“A ƙarƙashin jagorancinmu, mun samu yanayin aiki mai kyau da dangantaka mai kyau da gwamnati domin haɗin kai da zaman lafiya,” in ji Ukpoju.
Ya shawarci sabbin shugabanni su ci gaba da kula da zaman lafiya da haɗin kai don walwalar mambobi.
