ADC: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar Nafiu Bala akan Mark da Aregbesola

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da Nafiu-Bala Gombe ya shigar, wadda ya ke neman a hana shugabannin ADC  da Daɓid Mark ke jagoranta, ci gaba da gabatar da kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar, zuwa ranar 28 ga watan Satumba.

An sanya ranar Litinin domin sauraron dukkan ƙorafe-ƙorafen da ke gaban kotun dangane da ƙarar, sai dai zaman bai yiwu ba saboda Alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Peter Lifu, bai zauna ba.

Daga bisani, kotun ta sanya ranar 28 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraron shari’ar.

A ranar 16 ga watan Yuni, Mai Shari’a Lifu ya sanya ranar sauraron dukkan ƙorafe-ƙorafen da ke gaban kotun, bayan da ya yi watsi da buƙatar da aka gabatar ta neman ya janye daga shari’ar.

Alƙalin ya ce buƙatun biyu da jam’iyyar ADC da Ogbeni Rauf Aregbesola, waɗanda suke a matsayin wanda aka ƙara na farko da na uku, suka gabatar, ba su da hujjar da za ta sa a amince da su.

Saboda haka, ya ci tarar ADC da Aregbesola Naira miliyan ɗaya kowannensu, inda kuɗin za su tafi ga Nafiu-Bala Gombe.

ADC da Aregbesola sun gabatar da buƙatu daban-daban ga Mai Shari’a Lifu, suna neman ya janye daga sauraron ƙarar da Gombe ya shigar, bisa zargin cewa yana nuna son kai a shari’ar.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, NAN, ya ruwaito cewa Gombe, a cikin ƙarar, yana neman kotu ta bayar da umarnin da zai hana Daɓid Mark, Aregbesola da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar, National Working Committee (NWC), ci gaba da gabatar da kansu a matsayin shugabannin ADC.

Gombe ya yi zargin cewa yadda Mark, Aregbesola da sauran mambobin kwamitin rikon kwaryar suka samu shugabancin jam’iyyar ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ADC da kuma dokar zaɓe.

Gombe ya shigar da ƙarar ne kan ADC, Daɓid Mark, Rauf Aregbesola, Hukumar INEC da Ralph Nwosu, waɗanda aka ambata a matsayin waɗanda ake ƙara na farko zuwa na biyar, a cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025.

Ralph Nwosu shi ne tsohon shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, wanda ya sauka daga mukaminsa domin bai wa shugabancin jam’iyyar da Daɓid Mark ke jagoranta damar hawa.

By ukarofi

Leave a Reply