Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar nan, maimakon shiga rigingimun siyasa da jam’iyyun adawa.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaranta na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, inda ta mayar da martani kan kalaman da Shugaba Tinubu ya yi na cewa a shirye yake ya yi “faɗan ƙarshe” a fagen siyasa.
A cewar ADC, bai kamata shugaban ƙasa ya fi mayar da hankali kan fafatawa da ‘yan adawa ba, alhali ƙasar na ci gaba da fuskantar barazanar ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Jam’iyyar ta yi nuni da harin da aka kai ƙauyen Naridon da ke ƙaramar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, tana mai cewa irin waɗannan hare-hare su ne ya kamata gwamnatin tarayya ta fi mayar da hankali wajen daƙilewa.
ADC ta kuma yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta fi yawan fitar da sanarwar Allah-wadai da ta’aziyya bayan hare-hare, maimakon ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Jam’iyyar ta jaddada cewa ‘yan Nijeriya sun zaɓi Shugaba Tinubu ne domin ya magance matsalar rashin tsaro, yaƙi da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, ba domin ya shiga takun-saƙa da jam’iyyun adawa ba.
Haka kuma, ta yi iƙirarin cewa shugaban ƙasar ya fi mayar da martani ga ‘yan adawa fiye da yadda yake mayar da hankali wajen warware matsalolin tsaro da suka addabi al’umma.
ADC ta ce duk da shekaru da gwamnatin ke yi a kan mulki, har yanzu ana ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda da sauran masu aikata manyan laifuka a sassa daban-daban na ƙasar.
A ƙarshe, jam’iyyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara himma wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tana mai jaddada cewa ana samun nasarar zaɓe ne ta hanyar kyakkyawan aiki da ingantaccen shugabanci, ba ta hanyar kalaman nuna ƙarfi a siyasa ba.
