Ahmed Musa ya shirya komawa Kano Pillars – Rahoto

Daga WAKILINMU

Rahotanni sun tabbatar cewa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan kuma kyaftin a Super Eagles, wato Ahmed Musa, na shirin sake komawa ƙungiyar Kano Pillars don yin aiki na taƙaitaccen lokaci.

Musa, ɗan shekara 28, ya kasance ba ya buga ma wata kulob wasa tun daga Otoban 2020, bayan kammala harƙallarsa da ƙungiyar Al Nassr ta ƙasar Saudiyya, bayan kuma ya kasa samu ƙulla wata harka a Turai.

Bayanai sun nuna ana sa ran tsohon ɗan wasan Leicester City ɗin zai yi aiki na ɗan lokaci tare da Kano Pillars.

Kanawa na matuƙar martaba ɗan wasan tun bayan da ya zira ƙwallaye goma sha takwas a raga yayin kakan wasa na 2009/2010 wanda hakan ya haifar masa da samun matsayin ɗan wasan da ya fi kowanne zira ƙwallaye a raga sannan Kano Pillars ta zama ta biyu yayin gasar albarkacin haka.

A halin da ake ciki, Kano Pillars ƙarƙashin jagorancin kocinta Ibrahim Musa Jugunu, ita ce ta biyu a jadawalin NPFL, inda ake sa ran zuwan Ahmed Musa zai taimaka wa ƙungiyar wajen lashe gasar wannan kaka.