Hajjin 2021: An yi wa maniyyata 2,837 rigakafin korona a Kaduna

Daga WAKILINMU

A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajjin bana, Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Jihar Kaduna ta ce kawo yanzu an samu yi wa maniyyata 2,837 allurar rigakafin cutar korona a jihar.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugabar Riƙon Ƙwarya ta Hukumar, Hannatu Zailani, a wata ganawa da ta yi da manema labarai, tana mai cewa an soma gudanar da shirin yi wa maniyyatan rigakafin ne tun ran 6 ga Afrilun da ake ciki.

Hannatu ta ce daga cikin maniyyata sama da 4,000 da jihar ke da su a bana, mutum 2,837 ne suka je suka karɓi allurarsu. Tare da bada tabbacin za a kammala shirin rigakafin a wannan makon.

A cewarta an gudanar da shirin rigakafin ne domin cika umarnin Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) wadda ta buƙaci dukkan jihohi su yi wa maniyyatansu rigakafin korona.

Kana ta jaddada cewa babu wani maniyyacin jihar da zai tafi aikin Hajjin bana ba tare da ya yi wannan rigakafin ba.