Kebbi: Wasu jigogin APC sun buƙaci a yi karɓa-karɓa game da kujerar gwamna

Daga FATUHU MUSTAPHA

Wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Kebbi, sun yi motsi tare da ɗauko batun karɓa-karɓa game da sha’anin shugabancin jihar a tsakanin shiyoyin jihar.

Da yake yi wa manema labarai bayani jim kaɗan bayan kammala ganawa da masu faɗa a ji na APC daga shiyoyin sanata na Kudu da Arewa na jihar, mai magana da yawun haɗakar kuma Kwamishinan Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Mohammed, ya ce manufarsu ita ce yadda za a tafi da kowa amma babban burinsu shi ne yadda za a riƙa kewayawa da keuerar gwamna ana karɓa-karɓa daga wannan mazaɓar sanata zuwa waccan don kowane ɓangare ya samu ya taɓa.

“Burinmu shi ne neman adalci ta yadda za a sakar wa sauran shiyyoyi su ma su taɓa mulkin jiha.”

Tare da buga misali da gwamnatin Neja inda ya ce ana kwatanta irin abin da suke fatan jiharsu ma ta yi koyi da shi.

Kazalika, haɗakar ta yi kira ga Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Ƙasa, Abubakar Malami SAN, da ya fito ya nemi muƙamin shugaban ƙasa ko na mataimakinsa amma kujerar gwamnan Jihar Kebbi ba.

A cewar Mohammed, “Ko sau guda babu inda Malami ya fito kai tsaye ko a fakaice ya nuna kwaɗayin neman muƙamin gwamnan Kebbi, amma a matsayinsa na mutum na uku a Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, muna ganin abin da ya fi dacewa shi ne ya nemi can sama.

“Muddin za mu yi masa adalci, kamata ya yi mu yi masa addu’ar alheri, sannan ya zuwa 2023 mu ba shi damar zama shugaban ƙasa ko mataimakinsa amma ba wai a haɗa shi da muƙamin gwaman jihar Kebbi ba.”