Aikata rashawa: Za mu cafke wasu gwamnoni da zarar sun sauka daga kan mulki – EFCC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana cewa, ta kammala shirye-shiryen kama tare da hukunta wasu gwamnonin da wa’adin mulkinsu ke ƙarewa waɗanda ake zargi da ayyukan rashawa.

Hakazalika, EFCC ɗin bayyana shirinta na kama wasu gurɓatattun masu riƙe da muƙaman gwamnati bayan miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaban EFCC, Mista Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka ranar Alhamis yayin tattaunawa da manema labarai.

Sai dai Bawa bai bayyana sunaye ko kuma yawan waɗanda suke shirin kamawa ba da zarar sun sauka daga kan mulki.

A sane cewa a bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya dai, gwamnoni na cikin jami’an gwamnati da ke da kariya wadda ya hana a kama su idan suna kan mulki.

Shugaban na EFCC ya ce akwai ma’aikatun gwamnati guda biyu da hukumar ke bincike a kansu a halin yanzu saboda ayyuka da suka saba wa ƙa’ida da su ke yi.

A cewarsa, a ɗaya daga cikin ma’aikatun an yi almundahanar kuɗafe ta Naira biliyan 4 na wasu kwangiloli kusan 20.

Bawa ya ce, “A yanzu haka, muna binciken ma’aikatu biyu da aka biya kuɗaɗen har sau biyu a cikinsu.

“Waɗannan kwangiloli ne da aka yi tun shekarar 2018, sannan wasu mutane masu ƙarfin hali suka fito da suka bayyana batun.

Ya ce, an buga takardun bogi a cikin ma’aikatun, sannan da hadin-bakin wasu ma’aikata, aka ƙirƙiri takardun karya tare da biyan kuɗi.

Bawa ya ce, muddin aka mayar da harkokin gwamnati ta hanyar zamani, ba za a samu irin waɗannan badaƙaloli ba.

Ya kuma mayar da martani kan wasu ƙungiyoyin farar hula da aka samu suna neman a kore shi, yana mai cewa hukumar ba za ta firgita ba ballantana hakan ya sa ta yi ƙasa a gwiwa.