‘Yan Shi’a sun koka da ci gaba da tsare Sheikh El-Zakzaky

Daga SANI AHMAD GIWA

Ƙungiyar Harkar Musulunci a Nijeriya, wato Shi’a, ta sake kokawa kan ci gaba da tsare shugabansu, Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky.

A cewar ƙungiyar, shugabansu ba shi da cikakkiyar lafiya a lokacin da yake tsare, wanda shi ne babban dalilin da ya sa suka fara muzaharar ‘Free Zakzaky’ a Abuja.

Idan dai ba a manta ba, duk da wasu hukunce-hukuncen da kotuna suka yanke na bayar da umarnin sakin jagoran da matarsa ​​Zeenat Ibraheem ba tare da wani sharaɗi ba, gwamnatin Buhari na ci gaba da tauye musu haqqinsu ta hanyar sanya musu takunkumin tafiye-tafiye tare da ƙwace fasfo na fita ƙasashen waje.

A nata muhawara, ƙungiyar ta ce hukuncin da babbar kotun Kaduna ta yanke na sallamar malamin da mai ɗakinsa tare da wanke su, ya ba su damar tafiya neman lafiya, tana mai cewa gwamnatin Buhari ta yi watsi da hukuncin kotun inda ta umurci babban lauyan gwamnatin tarayya, Hukumar Leƙen Asiri ta Qasa (NIA), DSS, da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) don ci gaba da riƙe fasfo ɗin fita ƙasashen duniya na babban malamin da matarsa.

Wannan sabon kiran yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai mai ɗauke da kwanan wata 24 ga Maris, 2023 mai ɗauke da sa hannun Fatima Aliyu Adam ta ƙungiyar Academic Forum na Harkar Musulunci a Nijeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Jama’a za su tuna cewa a ranar 2 ga Disamba, 2016, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin a saki Sheikh El-Zakzaky da matarsa ​​ba tare da wani sharaɗi ba.”

Har ila yau, a ranar 5 ga watan Agusta, 2019, babbar kotun Jihar Kaduna ta bayar da umarnin a saki malamin da matarsa domin su je su yi jinya a wani asibitin Indiya, wanda gwamnatin Buhari ta qi amincewa.

“A ranar 24 ga Fabrairu, 2020, babbar kotun Kaduna ta kuma tabbatar da cewa ma’auratan ba su cancanci a yi musu shari’a ba, don haka aka bada umarnin cewa jami’an gidan yarin na Kaduna da su ba su damar ganin likitocinsu, amma duk abin ya ci tura.

“Haka kuma, a ranar 28 ga Yuli, 2021, babbar kotun Kaduna ta saki tare da wanke ma’auratan daga dukkan zarge-zargen da ake yi musu.

“Ya kamata jama’a su lura cewa Sheikh Zakzaky da matarsa ​​suna da matsaloli da dama da ke barazana ga lafiyarsu, sakamakon kisan kiyashin da aka yi a Zariya, kuma har ya zuwa yanzu akwai harsasai da dama a jikinsu, kuma burbushin harsashi ya bar guba a jikin shi.

Halin lafiyar Sheikh El-Zakzaky da matarsa ​​ba wai samun ƙwararrun likitoci ba ne kawai, har ma da wurin kiwon lafiya da kayan aiki na zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *