Mutum 21 sun mutu a hatsarin mota a hanyar a Maiduguri

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Wata mota ƙirar Hummer mai laba JMA 59 XA, wadda ta taso daga garin Hadejia zuwa Maiduguri ta yi haɗari wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutum 21.

Lamarin ya faru ne a garin Udubo da ke Ƙaramar Hukumar Gawama, Jihar Bauchi, bayan da tayar gaban motar ta fice, hakan yasa direban motar rikicewa nan take ta doke mutane huɗu dake gefen titi ta kuma kama da wuta.

Bayan zuwan jami’an ‘yan sanda wurin, sun ɗauki mutum huɗu da suka ji raunuka da gawarwakin mutum 21 zuwa FMC da ke Azare.

Daga nan ne aka kwashi gawarwakin zuwa babban asibitin Hadejia inda aka yi musu sallah tare da bada cigiyar ‘yan uwan mamatan.

Lamarin ya tada hankalin al’ummar garin Hadejia da ma na Ubudo ganin yadda hatsarin ya munana.

A ƙarshe, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi, CP Aminu Alhassan Psc, ya jajanta wa ‘yan uwan mamatan tare da roƙa musu gafarar Ubangiji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *