Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Talata ya ayyana kujerun Sanata uku a matsayin babu kowa biyo bayan rasuwar mambobin Majalisar Dattawa ta 10.
Mazaɓun da abin ya shafa sun haɗa da Enugu ta Arewa, Nasarawa ta Arewa, da Ribas ta Kudu maso Gabas.
Mista Akpabio ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisa, inda ya ce guraben sun samu ne sakamakon rasuwar sanatocin da ke wakiltar waɗannan yankuna, bisa tanadin kundin tsarin mulki.
“Saboda waɗannan abubuwan bakin ciki da suka faru ga Majalisar Dattawa ta 10, an samar da gurabe domin gudanar da zaɓen cike gurbi ta hannun Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) domin a cike guraben da rasuwar abokan aikinmu ta haifar,” inji shi.
Yana mai yin nuni da Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), Shugaban Majalisar Dattawan ya ayyana kowace kujera a hukumance a matsayin babu kowa.
“Na ayyana kujerar Sanatan Enugu North a matsayin babu kowa. An ayyana kujerar a matsayin babu kowa,” inji shi, kafin ya yi irin wannan sanarwa ga Nasarawa North da Ribas South-East.
Daga nan ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da ta gudanar da zaɓen cike gurbi domin cike waɗannan kujeru cikin wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada.
“Bisa tanadin kundin tsarin mulkinmu, an ɗora wa INEC alhakin gudanar da sabbin zaɓe domin cike waɗannan kujerun Sanata cikin lokacin da aka ƙayyade, wanda kusan kwanaki 30 ne daga wannan sanarwa,” inji Akpabio.
Wannan ci gaba ya buɗe ƙofa ga sabbin fafatawar zaɓe a waɗannan mazabu, yayin da ake sa ran jam’iyyun siyasa za su fara shirin tattara ƙarfi kafin zaɓen cike gurbin domin cike kujerun Majalisar Dattawa.
