Al’ummar Nufawa da kafuwar Masarautar Nufe a Nijeriya (II)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamar yadda jaridar Blueprint Manhaja ta fara kawo wa mai karatu tarihin asalin Ƙabilar Nufawa a makon da ya gabata, a wannan makon za ta cigaba daga inda ta tsaya.

Masarautar Bida ta zama ta farko a lokacin Turawan mulkin mallaka, a lokacin ’yancin kan Nijeriya sarakunan ƙasar Bida sun ba da gudunmawa wajen haskaka bikin ’yancin ƙasar nan.

Har zuwa yau, masarautar Bida na shirya bikin gargajiya da ake wa laƙabi da ‘Nupe Cultural Day’ don tunawa da gudunmawar da sarakunan masarautar suka bayar da ake wa laƙabi da ‘Etsu’.

Sarakunan ƙasar Nufe daga shekarar 1531 zuwa 1835:
Tsoede, wanda ya kafa masarautar Nufe a shekarar 1531-1591, haifaffen da ne ga Attah na Iddah, bayan shi sai Edegi ko Choede Shaba wanda ya jagoranci masarautar a shekarar 1591 zuwa 1600, daga nan sai Tsoacha.

Zaulla ya jagoranci masarautar Nufe a shekarar 1600 zuwa 1625. Bayan shi kuma sai Zabunla ko Zagulla Jiga a shekarar 1625 zuwa 1670, sai Jia ko Jigba Mamman Wari ya karɓa a shekarar 1670 zuwa 1679. Abdu Waliyi ya jagoranci masarautar a shekarar 1679 zuwa 1700, sannan Aliyu a shekarar 1700 zuwa 1710.

Ganamace ya zama sarki a shekarar 1710 zuwa 1713, haka kuma Sachi Gana Machi Ibrahima ya yi sarauta daga 1713 zuwa 1717, sai kuma Idrisu daga I1717 zuwa 1721.

Ederisu Tsado ya yi sarauta daga 1721 zuwa 1742, haka kuma tarihi ya nuna cewar Chado ko Abdullahi Abubakar Kolo ya yi sarauta daga 1742 zuwa 1746, sai kuma Jibrin ya karva daga 1746 zuwa 1759, daga nan kuma Jibrilu Ma’azu ya yi mulki daga 1759 zuwa 1767, Majiya ya karɓa daga 1767 zuwa 1777, Malam Zubeiru Iliyasu daga 1777 zuwa 1778.

Ma’azu ya karɓa daga shekarar 1778 zuwa 1795. Daga nan kuma sai Alikolo Tankari daga shekarar 1795 zuwa 1795, Malam Mamma daga 1795 zuwa 1796, sai Malam Jimada ya karva daga 1796 zuwa 1805.

A shekarar 1796 yaqi ya varke tsakanin Malam Jimada da Majiya na II (jikokin Iliyasu), wanda ya janyo masarautar ta dare gida biyu tsakanin gabas da yamma har zuwa wani ƙayyadajjen lokaci, Malam Jimada na mulkin yankin gabas har zuwa rasuwarsa a shekarar 1805.

Malam Majiya na II ya mulki ɓangaren arewa daga 1796 zuwa 1810. An cigaba da tafiyar da mulkin ɓangaranci tun bayan rasuwar Malam Jimada a shekarar 1805, Mulkin Nufe ya tabbata har zuwa mutuwar Jimada a shekarar 1805, sai bayan zuwan Etsu Idrisu na II a shekarar 1810 zuwa 1830. Majiya na II ya cigaba da mulki daga shekarar 1830 zuwa 1834. Bayan zuwan Etsu Tsado a shekarar 1834 zuwa 1835 masarautar ta kasance ƙarƙashin Daular Fulani.

Masarautar Nufe daga shekarar 1835 zuwa 1901:
Usuman Zaki ɗan Malam Dendo ya Mulki masarautar daga 1835 zuwa 1841, sai Masaba ɗan Malam Dendo daga shekarar 1841 zuwa 1847 da shi kuma Umar Bahaushe daga 1847 zuwa 1856. Usuman Zaki ɗan Malam Dendo 1856 zuwa 1859 (a karo na biyu). Masaba ɗan Malam Dendo daga 1859 zuwa 1873 (a zango na biyu). Umaru Majigi ɗan Muhamman Majigi ya yi Mulki daga shekarar 1873 zuwa 1884, daga nan sai Maliki ɗan Usman Zaki daga 1884 zuwa 1895, sai Abu Bakr ɗan Masaba daga 1884 zuwa 1895 wanda ya rasu a 1919.

Muhammadu ɗan Umaru Majigi ya yi Mulki daga 1895 zuwa 1901 a lokacin ne masarautar ta kasance cikin tsarin sarakunan Arewa.

Masarautar Bida daga shekarar 1901 zuwa yau:
Muhammadu ɗan Umaru Majigi ya mulki masarautar daga shekarar 1901 cikin Fabrairu zuwa 1916, bayan shi sai Malam Bello ɗan Maliki daga ranar 6 ga Maris na shekarar 1916 zuwa 1926. Sai kuma Malam Sa’idu ɗan Mamudu daga Fabrairun 1926 zuwa 1935, daga nan Malam Muhammadu Ndayako dan Muhammadu daga ranar 28 ga Fabrairun shekarar 1935 har zuwa 29 ga watan Oktoban 29 1962.

Daga shi kuma sai Usman Sarki ɗan Malam Sa’idu daga 29 ga Oktoban 1962 zuwa 1969, ya rasu a shekarar 1984. Malam Musa Bello ya hau karagar masarautar a shekarar 1969 zuwa ranar 10 ga Janairun shekarar 1975. Sai Mai martaba Umaru Sanda Ndayako da ya mulki masarautar daga 1975 zuwa rasuwarsa a shekarar 2003. Bayan rasuwarsa, aka naɗa mai martaba Dakta Yahaya Abubakar a matsayin Etsu Nupe na 13 a ranar 11 ga watan Satumbar 2003 har zuwa yau. Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon rai a karagar mulkin masarautar da ke Bida.

Garin Bida da ke Ƙaramar Hukumar Bida a Jihar Neja, wacce ta mamaye yankin ƙaramar hukumar:
Ƙaramar hukumar mai girman kilomita 51, tana da yawan al’umma da suka kai adadin yawan 188,181 a ƙidayar shekarar 2006, wadda ke da lamba 912 na yankunan ƙasar nan na garuruwan ƙananan hukumomi.

Garin wanda ya shahara wajen saka kayan gargajiya, an shaidi garin Bida da shirya bukukuwan Sallah. Kuma a nan ne Kwalejin Kimiyya ta gwamnatin tarayya ta ke, kuma a nan ne cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya da kuma makarantar koyon aikin jinya mallakin gwamnatin jiha su ke.

Bida ita ce hedikwatar Nufawa, wanda Etsu Nupe na yanzu Dakta Yahaya Abubakar ke sarauta. Tsarin sarautar su ta saraki ne da ake yi wa laƙabi da ‘Etsu Nupe’. Kasancewar masarautar Allah ya azurta ta kuma tana rungumar baƙi, akwai ƙabilun Igbo, Yarbawa da Hausawa da Gwari mazauna a cikinta.

Al’ummar Nufawa, suna da al’adu da dama, amma sakamakon jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo a ƙarni na 19 an samu sauyi, sai dai har zuwa yanzu wasu al’adun na nan daram.

Mafi yawan ƙabilar ba su watsar da al’adar tsaga a fuska ba, domin da shi ake gane asalin su da kuma zuri’ar da mutum ya fito a cikin ta domin kariya saboda canjin da zamani ke kawowa.
Kasancewar ƙirkire-ƙirkirensu na da ban sha’awa, Nufawa sun ƙware wajen sassaƙa itace ta hanyar kawatawa da kira don samar da kayyayyakin yau da kullum da kawa don girmamawa. Kamar yadda marubuci ‘Black Byzantium’ ya tabbatar.

Wasu Fitattun Masarautar:
Wasu daga cikin fitattun da suka taka rawar gani daga Nufawa, sun haɗa da; Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Marigayi Shaikh Ahmad Lemu wanda ya samu lambar yabo ta (OON, OFR), wanda ya rayu daga shekarar 1929 zuwa 2020. Sai mai shari’a marigayi Honarabul Jastis Idris Legbo Kutigi (OFR, GCON), da ya rayu daga 1934 zuwa 2018.

Akwai Mawallafin jaridar Bleuprint, Alhaji Mohammed Idris Malagi, Farfesa Muhammad Umaru Ndagi, da aka haifa a 1964. Sai fitaccen ɗan siyasa Shehu Ahmadu Musa, da ya rayu daga 1935 zuwa 2008. Sai kuma fitaccen ɗan siyasa Shaaba Lafiagi. Akwai fitaccen ɗan jarida kuma jagoran siyasa Suleiman Takuma, da ya rayu tsakanin 1934 zuwa 2001.

Har ila yau tarihi ba zai taɓa mantawa da Kakaki Nupe ba da ya kasance fitaccen marubuci, masanin harhaɗa magunguna wanda ya kafa kamfanin Jaridun LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, da ya rayu tsakanin 1962 zuwa 2020.

Sauran sun haɗa da Sanata Isa Mohammed Bagudu, da aka haifa a shekarar 1948, sai Sanata Zainab Kure, da Tsohon Gwamnan Neja, Injiniya Abdulkadir Kure, da ya rayu daga 1956 zuwa 2017. Sai kuma uba tsohon firimiyan Arewa na riqo Aliyu Makama, da ya rayu daga 1905 zuwa 1980.

Fitattun wakokinsu:
Ƙabilar Nufawa sun shahara da fice a waƙoƙin gargajiya na Ningba, na kiɗan Enyanicizhi, da waƙoƙin karramawa na Hajiya Fatima Lolo, da Alhaji Nda’asabe. Hajiya Nnadzwa, Hauwa Kulu da Baba-Mini da Ahmed Shata da kuma Ndako Kutigi, suna sahun gaba wajen daga harshen Nufanci saboda yaɗuwar waƙoƙinsu da soyayyarsu ga jama’a har ga waɗanda ba sa jin harshen Nufanchi.

Shahararrun ’yan wasan barkwanci:
Bayan zuwan wasannin barkwanci na zamani, an fara shirya wasanni gargajiya na Nufanci tun a shekarar 2000. Wanda ’yan asalin ƙabilar Nufawa suka assasa, ta hanyar shirya wasan barkwanci da harshen Nufanci, ba da umurni ga ’yan wasa. Marigayi Sadisu Muhammad DGN, Yarima Ahmed Chado, marigayi Husaini Kodo, M. B Yahaya da Jibrin Bala Jibrin ( Yikangi) su ne ginshiƙan ƙirƙira a harkar shirin Fim da harshen Nufanchi, wanda a yau ta zama masana’antar shirin Film da harshen Nufanci da ake wa laƙabi da ‘Nupewood’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *