Al’ummar yankin Hong Kong na ƙara jin daɗin rayuwarsu

Daga AMINA XU

Abokai, “Duniya a Zanen MINA” a yau na zana wani hoto game da zaman rayuwar jama’ar yankin Hong Kong bayan shekaru 25 da dawowar yankin ƙarƙashin ikon kasar Sin. Waɗannan tsoffi biyu a cikin zanena suna raye-raye cikin farin ciki, abin da ya bayyana halin da jama’ar yankin ke ciki. Ko kun san cewa, a cikin waɗancan shekaru 25 da suka gabata, yawan al’ummar yankin ya karu daga miliyan 6 da dubu 502.1 zuwa miliyan 7 da dubu 413.1, a yayin da matsakaicin tsawon rayuwar maza da mata ya ƙaru da shekaru 6.2 da ma 5.5, lamarin da ya sa Hong Kong ya zama daya daga cikin sassan duniya da aka fi samun tsawon rayuwar al’umma. Lallai zaman rayuwa cikin kwanciyar hankali da wadata da walwala, abu ne da ke taimaka wajen tabbatar da tsawon rayuwar jama’a.

Mai zane: Amina Xu