Abin dariya ne da ‘yan siyasar Birtaniya suka bada ra’ayinsu kan batun yankin Hong Kong

Daga CMG HAUSA

Yayin da aka cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong ƙasar Sin, firaministan kasar Birtaniya Boris Johnson da jami’in kula da harkokin waje da raya ƙasa na kasar Liz Truss sun ba da jawabi da sanarwa cewa, Birtaniya tana da alhakin kula da mazaunen yankin Hong Kong bisa haɗaɗɗiyar sanarwa a tsakanin Sin da Birtaniya, dake nuna cewa Birtaniya ba ta yi watsi da yankin Hong Kong ba. Wannan batun siyasa abin dariya ne, wanda ya shaida cewa, tsoffin ‘yan mulkin mallaka ba su son amincewa da haƙiƙanin yanayi na yanzu, wato ba su da ƙarfi kamar yadda suke da shi a lokacin baya, suna yunƙurin tsoma baki a harkokin yankin Hong Kong, har ma harkokin cikin gida na ƙasar Sin.

Gwamnatocin Sin da Birtaniya sun daddale haɗaɗɗiyar sanarwa a tsakaninsu a watan Disamba na shekarar 1984, don daidaita batun dawowar yankin Hong Kong ƙasar Sin, abu mafi muhimmanci shi ne Sin ta maido da ikon mulkin ƙasa a yankin. Bisa sanarwar, bayan da aka dawo da yankin Hong Kong a ƙasar Sin a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1997, ƙasar Birtaniya ba ta da ikon mulkin yankin da ikon tafiyar da harkokin yankin da kuma ikon sa ido kan yankin. Wato ƙasar Birtaniya ba ta da ikon tsoma baki a harkokin yankin na Hong Kong.

Akwai shaidu da dama dake bayyana yankin Hong Kong na samu ci gaba ko a’a, kamar irin yadda yankin ya zama yankin tattalin arziki mafi ‘yanci a duniya, da cibiyar hada-hadar kuɗi ta duniya, da cibiyar zirga-zirgar jiragen ruwa ta duniya, da kuma cibiyar yin ciniki ta duniya da sauransu. A cikin shekaru 25 bayan dawowar yankin, an samu manyan nasarori a yankin, kana an aiwatar da manufar “ƙasa ɗaya amma tsarin mulki biyu” a yankin cikin nasara.

A ƙasar Birtaniya kuwa, Scotland tana ƙoƙarin neman ‘yancin kai ta hanyar jin ra’ayoyin jama’a. Kana Ireland ta Arewa ita ma tana son ɓallewa daga Birtaniya. A lokacin, firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce, ba zai yi watsi da yankin Hong Kong ba, yunƙurinsa shi ne nuna ƙarfi ga waje da yin magana a duniya don sassauta matsalolin cikin ƙasar, yunkurin zai ci tura.

Yankin Hong Kong yanki ne na kasar Sin, ba shi da nasaba da ƙasar Birtaniya.

Fassarawar: Zainab