Shugaban Nijeriya ya yi maraba da isowar jirgin ruwan farko a tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki

Daga CMG HAUSA

Shugaban Ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi maraba da samun nasarar isar jirgin ruwan farko zuwa tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki, wacce ita ce tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta farko a ƙasar da ake gudanar da aikin gina ta a Lagos, cibiyar kasuwancin ƙasar.

Babban jirgin ruwan dakon kaya mai samfurin ZHEN HUA 28, ya taso ne daga yankin Hong Kong na ƙasar Sin, ya kuma isa kasar Najeriya a ranar Juma’a, wanda ke ɗauke da manyan injuna guda 3 da ake amfani da su wajen loda kayayyaki daga jiragen ruwa zuwa gabar teku, da wasu manyan injuna guda 10 da ake amfani da su wajen sauke kwantainoni daga cikin manyan jiragen ruwan dakon kaya a gabar teku, kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana ta bakin mai taimaka masa a fannin yada labarai Femi Adesina.

Shugaban Najeriyar ya taya murna ga dukkan masu ruwa da tsaki a fannin sufuri ta ruwan ƙasar, inda ya bayyana cewa, amincewa da ya yi na gina sabbin tashoshin jiragen ruwa guda hudu a ƙasar, ciki har da tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki, zai taimaka matuka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

A cewar sanarwar, matakin zai kuma taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi masu tarin yawa, da janyo jarin ƙasashen waje, da kuma ƙara azama kan yin kasuwanci cikin sauki a ƙasar.

Shugaba Buhari ya ƙara da cewa, amfanin teku da amfanin ruwa suna da matuƙar muhimmanci ga inganta zaman rayuwar al’ummar Najeriya, don haka a cewarsa, gwamnati za ta yi iyakar ƙoƙarinta wajen bunƙasa fannin don kyautata makomar fannin.

Fassarawar: Ahmad