Amaechi da Hayatudeen sun yi watsi da sakamakon zaɓen ADC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

’Yan takarar neman shugabancin ƙasa a jam’iyyar ADC, Mohammed Hayatudeen da Rotimi Amaechi, sun bayyana rashin amincewarsu da yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, inda suka yi zargin cewa an tafka maguɗi da kura-kurai a kusan duka sassan ƙasar.

Korafin nasu na zuwa ne yayin da jam’iyyar ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓen fidda gwani da aka gudanar domin tantance wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a babban zaɓen 2027.

Mohammed Hayatudeen, shi ne ya fara bayyana rashin amincewarsa da yadda aka gudanar da zaɓen.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na ɗ, Hayatudeen ya ce ya ba zai halarci taron sanar da sakamakon zaɓen saboda abin da ya kira “mummunan maguɗi da murɗe sakamako” da ya ce ya gani da idonsa a yayin gudanar da zaɓen.

“Ba zan halarci taron sanar da sakamakon zaɓen fidda gwani ba saboda yadda aka tafka maguɗi da murɗe sakamakon zaɓe a wasu jihohi,” in ji Hayatudeen.

Ya ƙara da cewa irin abubuwan da suka faru sun saɓa wa manufofin dimokuraɗiyya da adalci da jam’iyyar ta yi alkawarin tabbatarwa.

Daga bisani, tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Riɓers, Rotimi Amaechi, shi ma ya bayyana rashin amincewarsa da yadda aka gudanar da zaɓen.

Amaechi ya wallafa matsayinsa a shafinsa na ɗ da yammacin Talata, inda ya ce an samu kura-kurai da rashin gaskiya a wasu jihohi da suka shafi tsarin kaɗa ƙuri’a da tattara sakamako.

“Ba zan iya amincewa da tsarin zaɓen da aka gudanar ba saboda rahotannin maguɗi da rashin daidaito da suka fito daga wasu jihohi,” inji Amaechi.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, shugabancin jam’iyyar ADC bai fitar da wata cikakkiyar sanarwa ba dangane da ƙorafe-ƙorafen da ‘yan takarar biyu suka gabatar.

Jam’iyyar ADC ta zaɓi amfani da tsarin zaɓen kai tsaye (direct primary), inda aka bai wa mambobi damar kaɗa ƙuri’a a matakin mazaɓu da jihohi domin zaɓar ɗan takararta na shugaban ƙasa.

Rahotanni daga wasu jihohi sun nuna cewa an samu cunkoso, jinkiri wajen isar kayan zaɓe da kuma rikice-rikice kan jerin sunayen masu kaɗa ƙuri’a.

Duk da haka, magoya bayan jam’iyyar sun bayyana cewa zaɓen ya samu halartar jama’a sosai a wasu jihohin, musamman Legas, Kaduna, Kano da Adamawa.

Zaɓen fidda gwanin na ADC na ɗaya daga cikin mafi muhimmanci a tarihin jam’iyyar, musamman bayan yadda jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin kafa sabuwar gamayya domin ƙalubalantar jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) a zaɓen 2027.

Masu sa ido kan siyasa na ganin cewa yadda ADC za ta tafiyar da rikicin cikin gida bayan wannan zaɓe zai iya tasiri matuƙa wajen karɓuwar jam’iyyar a idon masu zaɓe.

By ukarofi

Leave a Reply