Kotu ta hana Mamuda Beverages samar da Pop Power saboda tambarin Fearless

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana kamfanin Mamuda Beverages Nigeria Limited ci gaba da samar da abin sha mai ƙara kuzari na ‘Pop Power’, bayan da kamfanin Rite Foods ya zargi kamfanin da kwaikwayon tambarin kayansa na ‘Fearless Energy Drink.’

Mai shari’a Justice Binta Nyako ce ta bayar da umarnin na wucin-gadi bayan ta yanke hukuncin cewa tsarin kwalin da tambarin Pop Power ke amfani da shi na da kamanceceniya sosai da na ‘Fearless’.

Kotun ta bayar da umarnin dakatar da samar da kayan nan take har sai an kammala sauraron shari’ar gaba ɗaya.

Haka kuma, kotun ta yi watsi da ƙorafin farko da kamfanin Mamuda Beverages ya gabatar, inda ta ce duk da sauya fasalin kayan, sabon ƙirar har yanzu tana kama da tambarin da Rite Foods Limited ta daɗe tana amfani da shi.

A ƙarƙashin umarnin kotun, za a gudanar da ƙididdigar duk kayayyakin “Pop Power” da aka riga aka samar ƙarƙashin kulawar kotu, sai dai an amince a ci gaba da rarraba waɗanda aka riga aka aera kafin hukuncin.

Kotun ta bayyana cewa umarnin hana samar da kayan zai ci gaba da aiki har zuwa ƙarshen shekarar nan ko kuma zuwa lokacin da aka kammala yanke hukunci a shari’ar.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Satumba domin ci gaba da shari’ar.

Rikicin ya samo asali ne daga ƙarar da Rite Foods ta shigar tun watan Janairun 2025, inda ta zargi Mamuda Beverages da ƙera wani samfurin da ke kwaikwayon kayanta duk da wata yarjejeniyar sulhu da aka cimma a wajen kotu, wadda ta tilasta wa Mamuda sauya fasalin kayan tare da guje wa karya haƙƙin tambari.

By ukarofi

Leave a Reply