Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tura jami’anta zuwa jihohi 15 da suke fuskantar barazanar afkuwar ambaliyar ruwa, da nufin wayar da kan al’umma da kuma ƙaura daga wurare masu haɗari.
Ta ce, waɗanda iftila’in ambaliyar ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta afkawa, ba su ɗauki gargaɗin hukumomi da muhimmanci ba kafin al’amarin ya zo musu.
Babban jami’in hulɗa da jama’a na NEMA, Manzo Ezekiel ya ce Jihohin sun haɗa da; Kogi, Imo, Enugu, Adamawa, Taraba, Borno, Zamfara, Katsina da Abuja.
Ya ce, mutanen da ambaliyar ranar 23 ga watan Mayu ta afka musu, sun gina gidajensu ne a wurare da ke da yiwuwar samuwar ambaliya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 200 da ɓatar wasu ɗaruruwa.
Tun da fari dai hukumar kula da yanayi ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a Abuja da wasu jihohi 14 ciki har da Neja, wadda akwai manyan madatsun ruwa guda uku da suka haɗa da Kainji, Jebba da Shiroro acikinta waɗanda suna bada gagarumar gudumawa ga rumbun wutar lantarki na ƙasa.
Neja a matsayinta na wadda ta fi kowace jiha faɗin ƙasa a Nijeriya ta fuskanci matsalolin ambaliya a ’yan shekarun nan, inda a watan Afrilu, ruwan da aka sako daga ɗaya daga cikin madatsun, ya yi sanadiyyar lalata gonaki sama da guda 5,000 da ƙauyuka 30 ciki har da Mokwa.
Haka ma a shekarar 2022, ambaliya sun yi sanadin rasa rayuka sama da 600 da ɗaiɗaita mutane kusan miliyan 1.4 da lalata filayen noma masu faɗin hekta 440,000.
A kan haka ne Gwamnatin Tarayya a ƙoƙarinta na shawo kan matsalar ambaliya, ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi da hukumomin agajin gaggawa.
