NCC ta umarci bankuna su fara cire kuɗin amfani da USSD a katin waya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta umarci bankuna da su dakatar da cire kuɗin tsarin amfani da waya don hada-hada, wato USSD kai tsaye daga asusun abokan hulɗarsu.

A cewar wata sanarwa da bankin UBA ya aika ga abokan cinikayyarsa a ranar Talata, ya ce a za a riƙa cire kuzin ne daga layin wayar hannunsu, ba daga asusun banki ba.

Wasu bankuna sun fara bin umarnin, inda UBA ya ce sabon tsarin ya fara aiki daga ranar Talata, 3 ga Yuni, 2025.

Wannan sabon umarni na iya zama wani yunƙuri daga NCC don warware rikicin biyan kuɗin USSD da ke tsakanin kamfanonin sadarwa da bankuna.

UBA ya shawarci abokan hulɗarsa da su ci gaba da amfani da sauran hanyoyin bankin zamani da tsarin intanet don samun saukin gudanar da hada-hada.

Sanarwar bankin ta ce, “Dangane da umarnin da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta bayar, ku sani cewa daga ranar 3 ga Yuni, 2025, ba za a ƙara cire kuɗin ayyukan bankin USSD daga asusun bankinku ba.”

“A maimakon haka, za a riƙa cire kuɗin daga katin wayarku, kamar yadda tsarin NCC na tanada.

A ƙarƙashin sabon tsarin biyan kuɗin, UBA ya bayyana cewa kowace mu’amala ta USSD za ta ciri Naira 6.98 a cikin kowane daƙiƙa 120, wanda kamfanin sadarwa ne zai cire daga kuɗin kiran waya.

Ya ce,” za a riƙa samun sako na neman amincewarka a duk lokacin da za a yi amfani da USSD, sannan za a cire kudin ne kawai idan ka amince da hakan.”

“Idan baka son ci gaba da amfani da USSD a ƙarƙashin wannan sabon tsarin ba, za ka iya dakatar da amfani da tashar USSD ɗin gaba ɗaya.”

A watan Disamba 2024, Babban Bankin Nijeriya (CBN) tare da NCC sun ba da umarni ga kamfanonin sadarwa da bankuna da su warware rikicin bashin Naira biliyan 250 na kuɗin USSD.

Kamfanonin sadarwa sun so dakatar da sabis saboda bashin da bankuna suka ci, wanda ya jawo NCC ta shiga tsakani domin tabbatar da an samu fahimtar juna.

By ukarofi