Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ƙaddamar da sabon littafi game da badaƙalar tallafin man fetur.
Littafin da Bawa ya rubuta ya yi bayani dalla-dalla kan yadda aka sace tare da wawure kuɗaɗe da sunan tsarin tallafin man fetur a Nujeriya.
Tsohon shugaban EFCC ya saka wa littafin suna ‘The Shadow of Loot & Losses: Uncovering Nigeria’s Petroleum Subsidy Fraud,’ kuma ya ƙunshi batun tallafin mai.
An fitar da wannnan littafi a hukumance a ranar 5 ga Yuni, 2025, ƙarƙashin Cable Books, wani sashe a kamfanin Cable Media and Publishing.
Haka nan kuma za a riƙa sayar da littafin a faɗin Nijeriya ta hannun shagon sayar da litattafai na Roving Heights Bookstore.
Bawa ya riƙe kujerar shugaban EFCC daga Fabrairu 2021 zuwa Yuni 2023, lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Kafin ya zama shugaban EFCC, Bawa ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu bincike a kwamitin musamman da EFCC ta kafa domin binciken badaƙalar tallafin man da ta kunno kai a shekarar 2012.
A cikin littafin, Bawa ya bayyana yadda aka wawure Biliyoyin Naira ta hanyar dabaru da dama kamar: Shigo da kaya na bogi, ƙarin kuɗin da babu cikakken bayani a kansu, Maimaita karɓar tallafi, Canja takardun shigo da kaya, Safarar mai zuwa ƙasashen waje
Tsohon shugaban EFCC ya ƙara da cewa, an yi amfani da waɗannan dabaru ne ta hanyar takardun bogi, rashin kulawa da haɗa baki tsakanin jami’an gwamnati da ’yan kasuwa.
A cewarsa, littafin ba kawai tona badaƙalar cin hanci da rashawa kaɗai ya yi ba, ya ankarar da mahukunta domin ɗaukar mataki da kuma riƙo da gaskiya a harkar tafiyar da kuɗaɗen jama’a a Nujeriya.
A ranar 29 ga Mayu, 2023, lokacin rantsar da shi, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da tuge tallafin man fetur.
Daga nan, farashin man fetur ya tashi daga N190 zuwa N500, har ya haura N1,000 kafin ya ɗan fara saukowa, wanda ya yanzu ake sayarwa kan N850 ko sama da haka.
