Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli, Farfesa Joseph Utseɓ, a Afrilu ne ya gabatar da hasashen ambaliyar ruwa na shekara ta 2025, wanda ya nuna cewa al’ummomi 1,249 a faɗin ƙananan hukumomi 176 a cikin jihohi 30 da Babban Birnin Tarayya Abuja za su iya faɗawa cikin matsalar ambaliya a shekarar 2025.
Jihohin da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) ta bayyana cewa suna da haɗarin ambaliya, sun haɗa da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Kuros Ribas, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo da kuma Jigawa.
Sauran sun haɗa da Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe and Zamfara.
“A bisa hasashen da aka yi, ana tsammanin al’ummomi 657 a yankunan 52 za su fuskanci babban haɗarin ambaliya tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni, 500 da 54 a ƙananan hukumomi 142 tsakanin Yuli da Satumba da kuma 484 a ƙananan hukumomi 56 daga Oktoba zuwa Nuwamba.
“An yi hasashen matsakaicin haɗarin ambaliya ga al’ummomi 445 a cikin ƙananan hukumomi 116 daga Afrilu zuwa Yuni, 1,458 a ƙananan hukumomi 271 daga Yuli zuwa Satumba, da kuma 1,473 a ƙananan hukumomi 171 tsakanin Oktoba da Nuwamba,” inji Ministan.
Matakan da ya kamata a ɗauka:
Da yake magana, shugaban tsangayar kimiyyar muhalli na jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi, Dokta Kante Pkantisawa, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su mai da hankali sosai kan hasashen yanayi da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMET) da NHSA suka yi.
Ya ce, “Ambaliyan da aka yi a Mokwa babban abin tunatarwa ne game da tasirin sauyin yanayi da kuma buƙatar ɗaukar matakan da suka dace, babu wata fa’ida cewa, a duk faɗin ƙasar nan, al’ummomi da masu ra’ayi dole ne su ƙara taka muhimmiyar rawa wajen hasashen yanayi da kamfanin NiMET ya yi da kuma hasashen ambaliyar ruwa na shekara-shekara da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya ta fitar a duk shekara.
“Har ila yau, yana da muhimmanci a gaggauta inganta magudanan ruwa da ake da su, tare da hanzarta samar da sabbin hanyoyin wucewar ruwa don rage ƙwararar ruwa da ɓarnar da ruwan ke haifarwa.”
Ya bayyana buƙatar bayar da shawarwari ga waɗanda suka rasa ‘yan uwa da kuma maido da rayuwar da ambaliyar ruwa ta lalata.
“Wannan lokaci ne na baƙin ciki ga iyalan waɗanda abin ya shafa, makwabtansu, da kuma al’ummarsu, zuciyata na tare da waɗanda suka rasa ‘yan uwansu, tare da dukiyoyinsu, gami da amfanin gona.
“Haka zalika, an lalata ababen more rayuwa sakamakon mummunar ambaliyar ruwa, ina addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya ji ƙan wazanda suka rasa rayukansu, ya kuma bai wa dangin su haƙurin rashi,” inji shi.
Hakazalika, wani mai fafutukar kare muhalli kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Dokta DuroRasak, ya bayyana ambaliyar Mokwa da ta faru a baya-bayan nan a matsayin “mummunan bala’i.” Ya yi kira ga hukumomi da su ƙara yawan kuɗaɗen da ake kashewa a fannin muhalli ga jihohin saboda tasirin sauyin yanayi.
“Ambaliyar ruwa da ta afku a garin Mokwa na jihar Neja a baya-bayan nan, wani abin tunawa ne mai ban tausayi game da illar rashin kula da muhalli da ababen more rayuwa, da rashin shirye-shiryen iftila’i da sauyin yanayi.
“Ambaliyar ruwan da ta afku a sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da ya fara tun a ranar 28 ga watan Mayu, ya yi sanadin asarar rayukan mutane da dama tare da jefa al’ummar Mokwa cikin firgici.
“Yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane sama da 200, wasu alƙaluma na nuni da cewa adadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa sosai, har zuwa 700, saboda yawancin waɗanda abin ya shafa sun shiga kogin Neja. Sama da mutane 3,000 ne suka rasa matsugunansu, gidaje sama da 265 sun lalace.
Ya ci gaba da cewa, “Baya ga mace-mace, ambaliya ta yi sanadiyyar raba dubban mutane da muhallansu, ta lalata gidaje da ɗaiɗaita rayuwa, tare da durƙusar da tattalin arzikin yankin.
“Yankuna da dama a Nijeriya ciki har da Mokwa na fama da rashin isassun kayayyakin more rayuwa na magudanar ruwa, magudanan ruwa da ake da su a lokuta da yawa suna cika da sharar gida, tare da hana ruwan wucewa yadda ya kamata.
Faɗakarwa:
A nasa ra’ayin, babbaa jami’iyar kula da shirin raya ƙasa na Majalisar ɗinkin Duniya, Cibiyar Muhalli ta Duniya, Shirin Ba da Tallafi (UNDP GEF SGP), Misis Ibironke Olubamise, ta buƙaci al’umma da su kasance cikin shiri, tare da ɗaukar darussa daga abubuwan da suka faru a baya, kuma kaɗa su yi la’akari da mummunar tasirin ambaliyar ruwa.
“Dole ne mu inganta dabarunmu kuma mu samar da tsare-tsare masu tsafta, gami da gano wasu hanyoyi,” inji ta.
A cewarta, hakan kuma zai taimaka wajen rage matsin lamba kan ayyukan bayar da agajin gaggawa idan ambaliyar ruwa ta afku.
Olubamise ya jaddada cewa Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA) za ta iya tallafa wa al’umma ta hanyar samar da kayan agajin gaggawa domin hasashen yiwuwar afkuwar ambaliya, maimakon jira har sai bala’i ya afku.
Har ila yau, wani malami a Sashen Tsare-tsare na Birane da Yanki na Jami’ar Olabisi Onabanjo, Oluwafemi Odunsi, ya ce tsare-tsaren birane da ake da su a Nujeriya sun tsufa, kuma sun bambanta da na zamani.
Odunsi ya yi nuni da cewa, ba a magance matsalar ambaliyar ruwa yadda ya kamata ba a manufofin da ake ciki yanzu, saboda babu wata dokar kula da ambaliyar ruwa ko kuma haɗewa tsakanin tsare-tsare na birane da tsare-tsaren rage haɗarin bala’i.
Har ila yau, shugaban ayyuka na ofishin NEMA na Lokoja, Musa Aliyu, ya shaida wa manema labarai cewa, hukumar ta ƙƙddamar da wasu shirye-shirye na wayar da kan jama’a da wayar da kan al’umma domin ƙarfafa matakan daƙile ambaliyar ruwa a faɗin jihar ta Kogi.
Ya ce ana kira ga al’ummar yankin da ƙungiyoyin masu gidaje da su fara share magudanun ruwa cikin gaggawa domin rage haɗarin ambaliya a birane.
“Mun fara kamfen na wayar da kan jama’a a duk faɗin yankinmu, yana da muhimmanci mazauna yankin su ɗauki matakin gaggawa, musamman ta hanyar share magudanan ruwa kafin damina ta tsananta,” inji shi.
