Amurka ta dakatar da kamfanonin Chana

Amurka ta dakatar da kamfanonin sarrafa wayoyi da sauran harkokin sadarwa na Chana da ke aiki a ƙasar, lamarin da ake ganin ba ya rasa nasaba da rikicin kasuwanci da gwada ƙarfin tattalin arziki a tsakanin ƙasashen biyu.

A cewar hukumomin Amurkan, sun yanke wannan shawara ce saboda ƙara inganta tsaro a Amurka musamman a rumbunan adana bayananta da ke fuskantar barazana daga Chana.

Amurka dai ta bai wa Hukumar Kula da Sadarwar Chana umarnin tabbatar da ficewar duk wasu kamfanonin da ke da alaƙa da samar da wayoyyi ko sadarwa da ke Amurkan cikin kwanaki 60, abin da ya kawo ƙarshen shekaru 20 na waɗannan kamfanoni a Amurka.

Ana dai ganin ɗaukar wannan matakin da Amurka ta yi wata hanya ce da ka iya rura wutar rikicin da ke ci a tsakaninsu ta ƙarƙashin ƙasa, saboda da ma ƙasashen sun jima ba sa jituwa dalilin kasuwanci.

Baya ga batun kasuwancin, ƙasashen na da rashin fahimta kan mamayar da Chana ke yi wa ƙasar Taiwan da Yankin Hong Kong, sai cin zarafin wasu al’ummar Musulmai a Chana da kuma batun ƙarfin saraffa kayayyakin fasaha.

Da alama shugaba Joe Biden ya gaji rashin jituwar da ke tsakanin Amurka da Chana daga tsohon shugaban ƙasar Donald Trump, wanda ake ganin irin yadda ya mu’amalanci Chana ƙarƙashin mulkinsa ne ya ƙarasa lalata alaƙar da ke tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *