Sanatocin Brazil sun nemi kotu ta dakatar da Bolsonaro daga kafafen zumunta

Wani kwamitin Majalisar Dattijan Brazil dake bincike kan matakan da gwamnatin ƙasar ta ɗauka wajen yaƙi da annobar Korona, ya buƙaci kotun ƙolin ƙasar da babban mai gabatar da ƙara, da su rufe shafukan shugaba Jair Bolsonaro na kafofin sadarwar zamani, saboda samunsa da laifin yin ƙarya wajen alaƙanta rigakafin Koronar da kuma kamuwa da cutar Sida.

Cikin buƙatar da suka mika ‘Yan majalisar Dattijan sun buƙaci kotun ƙoli da ta dakatar da shugaba Bolsonaro daga amfani da kafofin sadarwar zamanin da suka haɗa da ‘YouTube’ da ‘Twitter’ da ‘Facebook’ da kuma ‘Instagram’, bayan da bincike ya bankaɗo cewar shugaban na Brazil ya sharara ƙaryar cewa, wani rahoton gwamnatin Burtaniya ya gano cewar mutanen da aka yi wa allurar rigakafin Korona sun fi fuskantar hatsarin kamuwa da cutar Sida wato AIDS.

A cewar ‘yan majalisar na Brazil 11 dake cikin kwamitin binciken da ya shafe watanni shida yana aiki, ba za su iya ci gaba da lamuntar halayyar shugaban qasar nasu ba, don haka ya zama dole a ɗauki mataki akansa.

Kazalika, ‘yan majalisar sun nemi kotu da ta umurci Bolsonaro da ya yi jawabi ta kafar Talabijin ɗin ƙasar tare da janye iƙirarin ƙaryar da ya yi, in kuma yaƙi bin umarnin za a riqa cin tararsa dala 9,000 ko wace rana har zuwa lokacin da zai bi umurnin.

Kawo yanzu dai ƙididdiga ta nuna annobar Korona ta hallaka fiye da mutane 600,000 a Brazil, ƙasa ta biyu da annobar ta fi yi wa ta’adi a duniya bayan Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *